Mace ce bayan wata biyu tana biƙi, kuma bayan ta yi tsarki, sai ta fara samun wasu ɗige-ɗige ƙanana na jini, shin za ta sha, ba za ta yi sallah ba? ko kuma me za ta yi?
السؤال
TAMBAYA TA 1:
Mace ce bayan wata biyu tana biƙi, kuma bayan ta yi tsarki, sai ta fara samun wasu ɗige-ɗige ƙanana na jini, shin za ta sha, ba za ta yi sallah ba? ko kuma me za ta yi?
س24: امرأةٌ بعد شهرين من النّفاس، وبعد أن طهرت بدأت تجد بعض النّقاط الصغيرة من الدم، فهل تفطر، ولا تصلّي؟ أو ماذا تفعل؟
الجواب
AMSA TA 1:
Matsalolin mata a haila da biƙi kogi ne da ba shi da gaɓa, kuma yana daga cikin dalilansa, amfani da waɗannan ƙwayoyin masu hana ɗaukar ciki, da msau dakatar da haila, a da mutane ba su san waɗannan rikice-rikicen masu yawa ba.
Maganar ingantacciya ce cewar rikicin bai gushe ba akwai shi tun aiko Manzo - tsira da aminci su tabbata a gare shi - kai! tun ma farkon samuwar mace, saidai yawaitar sa a bisa wannan fuska da zai sa mutum ya tsaya a ruɗe wajen warware matsalolin sa lamari ne da.za a yi baƙin ciki a gareshi.
Saidai ƙa'ida gamammiya: Cewa idan mace ta yi tsarki, kuma ta ga tabbataccen tsarki a haila, ko a biƙi,- abin da na ke nufi da tsarki a haila: Shi ne fitar farar ƙassa, wadda ita wani ruwa ne fari, mata sun san shi- duk abin da ya biyo bayan tsarkin kamar ruwan hanta-hanta ko rawaya, ko dunƙule, ko danshi, duk wannan ba haila ba ne, ba zai hana sallah ba, ba zai hana azumi ba, ba zai hana saduwar miji da matarsa ba; sabo da ba haila ba ne,
Ummu Aɗiyya ta ce: Mun kasance ba ma lissafa [ruwan] fatsi-fatsi, da na hanta-hanta a matsayin wani abu. Bukhari ne ya fitar da shi, Abu Dawud ya yi ƙari: Bayan tsarki. Sanadin sa ingantacce ne.
A bisa wannan ne za mu ce: Duk abin da ya faru daga cikin waɗannan abubuwan bayan tsarki tabbatacce, to, ba za su cutar da mace ba, kuma ba za su hanata sallah da azumi da saduwar aure da miji ba, saidai yana wajaba, kada ta yi gaggawa har sai ta ga tsarki;
Sabo da wasu matan idan jini ya bushe musu, sai su yi gaggawa, su yi wanka, kafin su ga [cikakken] tsarki,
Sabo da haka matan sahabbai sun kasance, suna aikawa Uwar mummunai A'isha - Allah Ya yarda da ita - kursuf, yana nufin: Auduga da jini a jiki, sai ta ce da su: Kada ku yi gaggawa har sai kun ga farar kassa.
ﺟ24: مشاكل النّساء في الحيض والنّفاس بحرٌ لا ساحل له، ومن أسبابه: استعمال هذه الحبوب المانعة للحمل والمانعة للحيض، وما كان الناس يعرفون مثل هذه الإشكالات الكثيرة،
صحيحٌ أن الإشكال ما زال موجودًا من بعثة الرسول ﷺ، بل منذ وجد النّساء، ولكن كثرته على هذا الوجه الذي يقف الإنسان حيران في حلّ مشاكله أمرٌ يؤسف له.
ولكن القاعدة العامة: أن المرأة إذا طهرت، ورأت الطّهر المتيقن في الحيض وفي النّفاس -وأعني بالطّهر في الحيض: خروج القصة البيضاء، وهو ماءٌ أبيض تعرفه النّساء- فما بعد الطّهر من كدرةٍ، أو صفرةٍ، أو نقطةٍ، أو رطوبةٍ، فهذا كلّه ليس بحيضٍ، فلا يمنع من الصلاة، ولا يمنع من الصّيام، ولا يمنع من جماع الرجل لزوجته؛ لأنه ليس بحيضٍ، قالت أمّ عطية:
«كُنَّا لَا نَعُدُّ الصُّفْرَةَ وَالْكُدْرَةَ شَيْئًا»
أخرجه البخاريّ[1]، وزاد أبو داود [2]:
«بَعْدَ الطُّهْرِ»
وسنده صحيحٌ.
[6] كتاب الحيض، باب الصفرة والكدرة في غير أيام الحيض (326).
[7] كتب الطهارة، باب في المرأة ترى الصفرة والكدرة بعد الطهر (307).
وعلى هذا نقول: كلّ ما حدث بعد الطّهر المتيقن من هذه الأشياء فإنها لا تضرّ المرأة، ولا تمنعها من صلاتها وصيامها ومباشرة زوجها إياها، ولكن يجب ألّا تتعجل حتى ترى الطّهر؛
لأن بعض النّساء إذا جف الدم عنها بادرت، واغتسلت قبل أن ترى الطّهر،
ولهذا كان نساء الصحابة يبعثن إلى أمّ المؤمنين عائشة رضي الله عنها بالكرسف، يعني: القطن فيه الدم، فتقول لهن:
«لَا تَعْجَلْنَ حَتَّى تَرَيْنَ القَصَّةَ البَيْضَاءَ»[3].
[8] أخرجه البخاري معلقًا، كتاب الحيض، باب إقبال الحيض وإدباره.