Wasu matan jini yana zarcewa da su, wani lokaci yana yankewa kwana ɗaya ko biyu, sannan ya dawo, menene hukunci a wannan yanayin game da azumi da sallah da sauran ibadu?
- التصنيف الشرعي
- الفقهالصلاةمبطلات الصلاةالفقهالصيامأحكام الصيام
السؤال
TAMBAYA TA 1:
Wasu matan jini yana zarcewa da su, wani lokaci yana yankewa kwana ɗaya ko biyu, sannan ya dawo, menene hukunci a wannan yanayin game da azumi da sallah da sauran ibadu?
س25: بعض النّساء يستمرّ معهن الدم، وأحيانًا ينقطع يومًا أو يومين، ثم يعود، فما الحكم في هذه الحال بالنّسبة للصوم والصلاة وسائر العبادات؟
الجواب
AMSA TA 1:
Sanannen abu a wajen mafi yawan malamai cewa mace idan ya kasance tana da al'adarta, kuma al'adar ta ta ta ƙare, to, za ta yi wanka, za ta yi sallah, za ta yi azumi, abin da za ta gani kuma bayan kwana biyu ko uku ba haila ba ne; sabo da mafi ƙarancin tsarki a wajen waɗannan malamai shi ne kwana goma sha uku.
Wani sashin malamai kuma su ka ce: Duk lokacin da ta ga jini, to haila ne, kuma duk lokacin da ta samu tsarki, to, ita mai tsarki ce, ko da abin da ya ke tsakanin hailar guda biyu bai kai kwana goma sha uku ba.
ﺟ25: المعروف عند كثيرٍ من أهل العلم: أن المرأة إذا كان لها عادةٌ، وانقضت عادتها، فإنها تغتسل، وتصلّي، وتصوم، وما تراه بعد يومين أو ثلاثةٍ ليس بحيضٍ؛ لأن أقل الطّهر عند هؤلاء العلماء ثلاثة عشر يومًا.
وقال بعض أهل العلم: إنها متى رأت الدم فهو حيضٌ، ومتى طهرت منه فهي طاهرٌ، وإن لم يكن بين الحيضتين ثلاثة عشر يومًا.