Menene ya fi falala ga mace: Shin ta yi sallah a dararen Ramadan a gidanta, ko a masallaci, musamman ma idan ya kasance akwai wa'azuzzuka da tunatarwa? wacce faɗakarwa da za ka yi wa mata waɗanda suke sallah a masallatai?
السؤال
TAMBAYA TA 1:
Menene ya fi falala ga mace: Shin ta yi sallah a dararen Ramadan a gidanta, ko a masallaci, musamman ma idan ya kasance akwai wa'azuzzuka da tunatarwa? wacce faɗakarwa da za ka yi wa mata waɗanda suke sallah a masallatai?
س26: أيّهما أفضل للمرأة: أن تصلّي في ليالي رمضان في بيتها، أو في المسجد، وخصوصًا إذا كان فيه مواعظ وتذكيرٌ؟ وما توجيهك للنّساء اللاتي يصلّين في المساجد؟
الجواب
AMSA TA 1:
Abin da ya fi falala shi ne ta yi sallah a gidanta; sabo da gamewar faɗin Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -:
"Gidajensu su ne mafi alheri a garesu".
Kuma sabo da fitar mata ba ta rabuwa da fitina a mafi yawancin lokatai, kasancewar mace ta wanzu a gidanta, ya fi alheri a kan ta fita zuwa sallah a masallaci, wa'azuzzuka da hadisi za ta iya samunsu ta hanyar kaset.
Faɗakarwata ga matan da su ke yin a masallaci ita ce: Su dinga fita daga gidajensu zuwa masallaci ba tare da kwalliya da ado ba, kuma ba tare da shafa turare ba.
ﺟ26: الأفضل أن تصلّي في بيتها؛ لعموم قول النبيّ ﷺ:
«وَبُيُوتُهُنَّ خَيْرٌ لَهُنَّ» [1]،
ولأن خروج النّساء لا يسلم من فتنةٍ في كثيرٍ من الأحيان، فكون المرأة تبقى في بيتها خيرٌ لها من أن تخرج للصلاة في المسجد، والمواعظ والحديث يمكن أن تحصل عليها بواسطة الشريط.
[9] رواه أبو داود، كتاب الصلاة، باب ما جاء في خروج النساء إلى المساجد (567).
وتوجيهي للاتي يصلّين في المسجد: أن يخرجن من بيوتهن غير متبرّجاتٍ بزينةٍ، ولا متطيّباتٍ.