Skip to content

Idan mace ta samu tsarki, bayan sallar Asuba kai-tsaye, shin za ta kame ta ci gaba da azumin wannan ranar, sai ya zama ta samu ranar ta ta, ko kuma wajibi ne sai ta rama wannan ranar?

السؤال

TAMBAYA TA 1:

Idan mace ta samu tsarki, bayan sallar Asuba kai-tsaye, shin za ta kame ta ci gaba da azumin wannan ranar, sai ya zama ta samu ranar ta ta, ko kuma wajibi ne sai ta rama wannan ranar?

س1: إذا طهرت الـمرأة بعد الفجر مباشرةً فهل تمسك وتصوم هذا اليوم، ويكون يومها لها، أو عليها قضاء ذلك اليوم؟

الجواب

AMSA TA 1:

Idan mace ta samu tsarki bayan ɓullowar Alfijir, to, game da kamewarta malamai suna da maganganu biyu:

Magana ta farko: Cewa lallai ne sai ta kame a ragowar wannan wunin, sai dai cewa ba za'a lissafa mata da shi ba, kuma ramuwa ta wajaba a kanta, wannan ita ce magana shahararriya a Mazhabar Imam Ahmad - Allah Ya yi masa rahama -.

Magana ta biyu: Ba lallai ba ne sai ta kame a ragowar wunin; saboda wuni ne wanda azuminta baya inganta a cikinsa, sabo da kasancewarta mai haila a farkon sa, ba ta cikin masu azumi, idan kuwa bai inganta ba, kamewar ba ta da wani amfani, wannan lokacin lokaci ne ba mai wata alfarma ba a dangane da ita; sabo da ita abar umarta ce da ta sha a farkon ranar, kai haramun ne ma a gareta da ta azumci farkon wunin

Azumi na shari'a:shi ne, kamewa daga abubuwa masu karya azimi, domin bauta ga Allah -Ya girma Ya buwaya- daga ɓullowar alfijir har zuwa faɗuwar rana.

Wannan maganar - kamar yadda ka ke gani - ta fi rinjaye sama da maganar da take lazimtar kamewa, kuma abisa kowacce daga maganganun biyu ramuwar wannan wunin tana lazimtar ta.

ﺟ1: إذا طهرت المرأة بعد طلوع الفجر فللعلماء في إمساكها ذلك اليوم قولان:

القول الأول: أنه يلزمها الإمساك بقية ذلك اليوم، ولكنه لا يحسب لها، بل يجب عليها القضاء، وهذا هو المشهور من مذهب الإمام أحمد رحمه الله.

والقول الثاني: أنه لا يلزمها أن تمسك بقية ذلك اليوم؛ لأنه يومٌ لا يصحّ صومها فيه؛ لكونها في أوله حائضًا ليست من أهل الصّيام، وإذا لم يصح لم يبق للإمساك فائدةٌ، وهذا الزمن زمنٌ غير محترمٍ بالنّسبة لها؛ لأنها مأمورةٌ بفطره في أول النهار، بل محرمٌ عليها صومه في أول النهار،

والصوم الشرعيّ: هو الإمساك عن المفطّرات تعبّدًا لله عز وجل من طلوع الفجر إلى غروب الشمس.

وهذا القول -كما تراه- أرجح من القول بلزوم الإمساك، وعلى كلا القولين يلزمها قضاء هذا اليوم.