Idan mace ta kasance al'adarta ta wata-wata kwana takwas ne ko bakwai, sannan ta zarce da ita sau ɗaya ko biyu ko fiye da haka, to, menene hukuncin?
- الموضوعات
- الطهارةأحكام الحيض والنفاس
- التصنيف الشرعي
- الفقهالطهارةالحيض والنفاس والاستحاضة
السؤال
TAMBAYA TA 1:
Idan mace ta kasance al'adarta ta wata-wata kwana takwas ne ko bakwai, sannan ta zarce da ita sau ɗaya ko biyu ko fiye da haka, to, menene hukuncin?
س4: إذا كانت المرأة عادتها الشهرية ثمانية أيامٍ أو سبعة أيامٍ، ثم استمرت معها مرةً أو مرتين أكثر من ذلك، فما الحكم؟
الجواب
AMSA TA 1:
Idan al'adar wannan mata kwana shida ne ko bakwai, sannan lokacin ya yi tsawo, ya zama kwana takwas ko tara ko goma ko sha ɗaya, to, za ta zauna ba za ta yi sallah ba har sai ta yi tsarki.
Hakan kuwa sabo da Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - bai iyakance wata iyaka iyakantacciya a haila ba.
Haƙiƙa Allah - Maɗaukakin Sarki - Ya ce: {Kuma suna tambayar ka game da haila, Ka ce: Shi cũta ne} [Al-Baƙarah:222].
Duk lokacin da wannan jini ya wanzu, to, mace za ta tsaya a yadda ta ke har sai ta sami tsarki, ta yi wanka, sannan sai ta yi sallah, idan a wata na biyu ya zo mata ƙasa da haka, to, sai ta yi wanka idan ta yi tsarki, ko da bai kai tsawon lokaci na baya ba.
Abu mai muhummanci shi ne duk lokacin da ya zama akwai haila a tare da mace, to, ba za ta yi sallah ba, duk ɗaya ne; ko dai hailar ta kasance daidai da al adarta wacce ta gabata ne, ko kuma ta fi ta, ko kuma ta yi ƙasa da ita, idan ta samu tsarki sai ta yi sallah.
ﺟ4: إذا كانت عادة هذه المرأة ستة أيامٍ أو سبعةً، ثم طالت هذه المدة، وصارت ثمانيةً أو تسعةً أو عشرةً أو أحد عشر يومًا فإنها تبقى لا تصلّي حتى تطهر،
وذلك لأن النبي ﷺ لم يحد حدًّا معيّنًا في الحيض، وقد قال الله تعالى:
﴿وَيَسۡـَٔلُونَكَ عَنِ ٱلۡمَحِيضِۖ قُلۡ هُوَ أَذٗى...﴾
[البقرة:222]،
فمتى كان هذا الدم باقيًا فإن المرأة على حالها حتى تطهر، وتغتسل، ثم تصلّي، فإذا جاءها في الشهر الثاني ناقصًا عن ذلك فإنها تغتسل إذا طهرت وإن لم يكن على المدة السابقة.
والمهمّ أن المرأة متى كان الحيض معها موجودًا فإنها لا تصلّي، سواءٌ كان الحيض موافقًا للعادة السابقة، أو زائدًا عنها، أو ناقصًا، وإذا طهرت تصلّي.