Skip to content

Shin yana wajaba a kan mai biƙi ta yi azumi ta yi salla, idan ta samu tsarki kafin kwana arba'in?

السؤال

TAMBAYA TA 1:

Shin yana wajaba a kan mai biƙi ta yi azumi ta yi salla, idan ta samu tsarki kafin kwana arba'in?

س3: هل يجب على النّفساء أن تصوم وتصلّي إذا طهرت قبل الأربعين؟

الجواب

AMSA TA 1:

Eh, duk lokacin da mai biƙi ta samu tsarki kafin arba'in, to, ya wajaba a kanta ta yi azumi idan a Ramadan ne, yana wajaba a kanta ta yi sallah, ya halatta ga mijinta ya sadu da ita; saboda ita mai tsarki ce, babu wani abu a tare da ita, da zai hanata azumin, ko abin da zai hana wajibcin sallah da halaccin jima'i.

ﺟ3: نعم، متى طهرت النّفساء قبل الأربعين فإنه يجب عليها أن تصوم إذا كان ذلك في رمضان، ويجب عليها أن تصلّي، ويجوز لزوجها أن يجامعها؛ لأنها طاهرٌ ليس فيها ما يمنع الصوم، ولا ما يمنع وجوب الصلاة وإباحة الجماع.