Idan mai haila ta samu tsarki, ta yi wanka bayan sallar asuba, kuma ta yi salla, ta kammala azumin yininta, shin yana wajaba a kanta ta rama shi?
السؤال
TAMBAYA TA 1:
Idan mai haila ta samu tsarki, ta yi wanka bayan sallar asuba, kuma ta yi salla, ta kammala azumin yininta, shin yana wajaba a kanta ta rama shi?
س2: إذا طهرت الحائض، واغتسلت بعد صلاة الفجر، وصلت، وكملت صوم يومها، فهل يجب عليها قضاؤه؟
الجواب
AMSA TA 1:
Idan mai haila ta sami tsarki, kafin ɓullowar alfijir koda da minti ɗaya ne, kuma ta samu tabbacin tsarkin, idan ya kasance a Ramadan ne, to, azumin ya lazimce ta, kuma azumin ta na wannan ranar ya zamo ingantacce, ramuwar sa ba ya lazimtarta, sabo da ta yi azumi alhali tana mai tsarki, idan batayi wanka ba sai bayan ɓullowar alfijir, to, babu laifi.
Kamar yadda namiji da zai kasance mai janaba a sakamakon jima'i ko mafarki, sai kuma ya yi sahur, bai yi wanka ba, sai bayan ɓullowar alfijir, to, azumin sa ya inganta.
A wannan gaɓar, ina son in faɗakar game da wani lamari da ya shafi mata, shi ne, idan haila ta zo mata alhalin ta yi azumin ranar, wasu matan suna zaton cewa, idan haila ta zo mata bayan shan ruwa, kafin ta sallaci sallar Isha'i azumin ranar ya ɓaci.
Wannan ba shi da tushe, kai idan haila ta zo mata bayan faɗuwar rana koda da ƙifrawar ido ne, to azumin ta cikakke ne kuma ingantacce.
ﺟ2: إذا طهرت الحائض قبل طلوع الفجر ولو بدقيقةٍ واحدةٍ، ولكن تيقنت الطّهر، فإنه إذا كان في رمضان فإنه يلزمها الصوم، ويكون صومها ذلك اليوم صحيحًا، ولا يلزمها قضاؤه؛ لأنها صامت وهي طاهرٌ، وإن لم تغتسل إلا بعد طلوع الفجر فلا حرج،
كما أن الرجل لو كان جنبًا من جماعٍ أو احتلامٍ، وتسحر، ولم يغتسل إلا بعد طلوع الفجر، كان صومه صحيحًا.
وبهذه المناسبة أودّ أن أنبّه إلى أمرٍ آخر عند النّساء إذا أتاها الحيض وهي قد صامت ذلك اليوم، فإن بعض النّساء تظنّ أن الحيض إذا أتاها بعد فطرها قبل أن تصلّي العشاء فسد صوم ذلك اليوم،
وهذا لا أصل له، بل إن الحيض إذا أتاها بعد الغروب ولو بلحظةٍ فإن صومها تامٌّ وصحيحٌ.