Skip to content
Jerin Surori /

الكَهف

الكَهف is chapter 18 of the Quran and has 110 verses. This page presents it in full in the Uthmani script, with a verse-by-verse translation of its meaning.

110 Ayoyi Lambar Sura 18
Je zuwa aya
Hausa · Gummi
بِسْمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحْمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ

ٱلۡحَمۡدُ لِلَّهِ ٱلَّذِيٓ أَنزَلَ عَلَىٰ عَبۡدِهِ ٱلۡكِتَٰبَ وَلَمۡ يَجۡعَل لَّهُۥ عِوَجَاۜ

Gõdiya ta tabbata ga Allah wanda Ya saukar da Littafi a kan bãwansa kuma bai sanya karkata ba a gare shi.

قَيِّمٗا لِّيُنذِرَ بَأۡسٗا شَدِيدٗا مِّن لَّدُنۡهُ وَيُبَشِّرَ ٱلۡمُؤۡمِنِينَ ٱلَّذِينَ يَعۡمَلُونَ ٱلصَّٰلِحَٰتِ أَنَّ لَهُمۡ أَجۡرًا حَسَنٗا

Madaidaici, dõmin Ya yi gargaɗi da azãba mai tsanani daga gare shi, kuma Ya yi bushãra ga mũminai, waɗanda suke aikata ayyuka na ƙwarai da (cẽwa) sunã da wata lãdã mai kyau.

مَّٰكِثِينَ فِيهِ أَبَدٗا

Sunã mãsu zama a cikinta har abada.

وَيُنذِرَ ٱلَّذِينَ قَالُواْ ٱتَّخَذَ ٱللَّهُ وَلَدٗا

Kuma Ya yi gargaɗi ga waɗanda suka ce: "Allah yanã da ɗa."

Explanation & meanings · 1
  1. Lãrabawa sun ce malã'iku 'ya'yan Allah ne. Yahũdawa sunce Uzairu ɗan Allah ne, Nasãra sun ce Ĩsã ɗan Allah ne. Bãbu ladabi ga faɗin wannan magana. Sabõda haka Annabi Muhammadu, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya gaya musu, cewa wannan magana ƙarya ce kuma rashin ladabi ne ga Allah, da ba su yi ĩmãni ba, ya ji tsõro kada ya zama shĩ ne ya yi ƙwauron bãki ga faɗã musu gaskiya. Sai Allah Ya gaya masa, cewa kada ya halakar da ransa dõmin baƙin cikin haka.

مَّا لَهُم بِهِۦ مِنۡ عِلۡمٖ وَلَا لِأٓبَآئِهِمۡۚ كَبُرَتۡ كَلِمَةٗ تَخۡرُجُ مِنۡ أَفۡوَٰهِهِمۡۚ إِن يَقُولُونَ إِلَّا كَذِبٗا

Ba su da wani ilmi game da wannan magana, kuma iyãyensu bã su da shi, abin da ke fita daga bãkunansu ya girma ga ya zama kalmar faɗa! Ba su faɗan kõme fãce ƙarya.