18 : 83
وَيَسۡـَٔلُونَكَ عَن ذِي ٱلۡقَرۡنَيۡنِۖ قُلۡ سَأَتۡلُواْ عَلَيۡكُم مِّنۡهُ ذِكۡرًا
Kuma suna tambayar ka daga zulƙarnaini, ka ce: "Zan karanta muku ambato daga gare shi."
Explanation & meanings · 1
- Zulƙarnaini an ce sarki ne yanã bin shari'ar lbrãhĩm, ga hannunsa ya musulunta sunansa Askandar. Haliru wazirin sane yanã tafiya a gaban yãƙinsa, kuma ɗan innarsa, watau ɗan khãlarsa ne. Shi ne ya gĩna Askandariyya. Sai dai ga maganar akwai warware jũna. Allah Ya sani. Abin da ke a gabãninmu a nan shĩ ne sanin cħwa Allah Yã bã shi mulki, ya kõ yi shĩ bisa sharĩ'a, ya yi ƙarfi, da ƙarfin Allah.