Skip to content
Jerin Surori /

مَريَم

مَريَم is chapter 19 of the Quran and has 98 verses. This page presents it in full in the Uthmani script, with a verse-by-verse translation of its meaning.

98 Ayoyi Lambar Sura 19
Je zuwa aya
Hausa · Gummi
بِسْمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحْمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ

كٓهيعٓصٓ

K̃.H. Y.I. Ṣ̃.

ذِكۡرُ رَحۡمَتِ رَبِّكَ عَبۡدَهُۥ زَكَرِيَّآ

Ambaton rahamar Ubangijinka ne ga BawanSa Zakariyya.

إِذۡ نَادَىٰ رَبَّهُۥ نِدَآءً خَفِيّٗا

A lõkacin da ya kirãyi Ubangijinsa, kira ɓõyayye.

قَالَ رَبِّ إِنِّي وَهَنَ ٱلۡعَظۡمُ مِنِّي وَٱشۡتَعَلَ ٱلرَّأۡسُ شَيۡبٗا وَلَمۡ أَكُنۢ بِدُعَآئِكَ رَبِّ شَقِيّٗا

Ya ce: "Yã Ubangijina! Lalle ne nĩ, ƙashi na daga gare ni ya yi rauni, kuma kaina ya kunnu da furfura, kuma ban kasance marashin arziki ba game da kiranKa, yã Ubangiji!"

وَإِنِّي خِفۡتُ ٱلۡمَوَٰلِيَ مِن وَرَآءِي وَكَانَتِ ٱمۡرَأَتِي عَاقِرٗا فَهَبۡ لِي مِن لَّدُنكَ وَلِيّٗا

"Kuma lalle nĩ, na ji tsõron dangi a bãyãna, kuma mãtãta ta kasance bakarãriya! Sai ka bã ni wani mataimaki daga wajenKa."

Explanation & meanings · 1
  1. Amfãnin sãmu ɗã ga mutumin kirki shi ne dõmin ya gãji kirkin kuma ya taimaki sauran danginsa, ya rãyar da gida. Kuma wanda ba mutumin kirki ba yana yiwuwa ya sãmi ɗan kirki mai shiryar da shi zuwa ga hanyar ƙwarai.