Skip to content
الكَهف /

Aya 82

18 : 82

Aya 82 of الكَهف (18 : 82). This page carries the verse in the Uthmani script with a translation of its meaning, at a stable URL that can be cited on its own.

الكَهف Ayoyi 110
Sura · الكَهف
Hausa · Gummi
18 : 82

وَأَمَّا ٱلۡجِدَارُ فَكَانَ لِغُلَٰمَيۡنِ يَتِيمَيۡنِ فِي ٱلۡمَدِينَةِ وَكَانَ تَحۡتَهُۥ كَنزٞ لَّهُمَا وَكَانَ أَبُوهُمَا صَٰلِحٗا فَأَرَادَ رَبُّكَ أَن يَبۡلُغَآ أَشُدَّهُمَا وَيَسۡتَخۡرِجَا كَنزَهُمَا رَحۡمَةٗ مِّن رَّبِّكَۚ وَمَا فَعَلۡتُهُۥ عَنۡ أَمۡرِيۚ ذَٰلِكَ تَأۡوِيلُ مَا لَمۡ تَسۡطِع عَّلَيۡهِ صَبۡرٗا

"Kuma amma bangon, to, yã kasance na waɗansu yãra biyu ne, marãyu a cikin birnin, kuma akwai wata taska tãsu a ƙarƙashinsa, kuma ubansu ya kasance sahĩhin mutum ne, dõmin haka Ubangijinka Ya yi nufin su isa iyãkar ƙarfinsu, kuma sũ, su fitar da taskarsu, sabõda rahama ne daga Ubangijinka. Kuma ban yi shi ba daga umurnĩna. Wancan shĩ ne fassarar abin da ba ka iya yin haƙuri ba a kansa."

Explanation & meanings · 1
  1. Wannan ya nũna cewa kirkin uba yanã amfãnin ɗiyansa, haka gari na daraja sabõda sãmun mutãnen kirki a cikinsa, kamar yadda yake ƙasƙanta da ƙasƙancin mazaunansa bisa dalĩlin da farko an kira garin 'alƙarya' sabõda rõwar mazauna, kuma aka kira shi Madĩna sabõda darajar yãran nan biyu da ubansu da taskarsu. Alƙarya ita ce ƙaramin gari watau ƙauye, kuma Madĩna ita ce babban gari.