Skip to content
Jerin Surori /

الإسرَاء

الإسرَاء is chapter 17 of the Quran and has 111 verses. This page presents it in full in the Uthmani script, with a verse-by-verse translation of its meaning.

111 Ayoyi Lambar Sura 17
Je zuwa aya
Hausa · Gummi
بِسْمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحْمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ

سُبۡحَٰنَ ٱلَّذِيٓ أَسۡرَىٰ بِعَبۡدِهِۦ لَيۡلٗا مِّنَ ٱلۡمَسۡجِدِ ٱلۡحَرَامِ إِلَى ٱلۡمَسۡجِدِ ٱلۡأَقۡصَا ٱلَّذِي بَٰرَكۡنَا حَوۡلَهُۥ لِنُرِيَهُۥ مِنۡ ءَايَٰتِنَآۚ إِنَّهُۥ هُوَ ٱلسَّمِيعُ ٱلۡبَصِيرُ

Tsarki ya tabbata ga wanda Ya yi tafiyar dare da bãwanSa da dare daga Masallaci mai alfarma zuwa ga Masallaci mafi nĩsa wanda Muka sanya albarka a gefensa dõmin Mu nũna masa daga ãyõyinMu. Lalle ne Shi shĩ ne Mai ji, Mai gani.

Explanation & meanings · 2
  1. Isrã'i, shi ne tafiyar dare da Allah Ya yi da Annabi daga Makka zuwa Baitil Maƙadis. Sa'an nan Mi'iraji zuwa sama inda aka ba shi sallõli.
  2. Muƙarana a tsakãnin Masjidil Harãm watau tsararre daga a yãki mutãnensa da Masjidil Aƙsã wanda ba tsararre ba. Isrã'i da Mi'irãji sun fi Miƙãtin Mũsã da gãnãwarsa da Ubangiji a Ɗũr-Sĩna'a.

وَءَاتَيۡنَا مُوسَى ٱلۡكِتَٰبَ وَجَعَلۡنَٰهُ هُدٗى لِّبَنِيٓ إِسۡرَٰٓءِيلَ أَلَّا تَتَّخِذُواْ مِن دُونِي وَكِيلٗا

Kuma Mun bai wa Mũsã littafi, kuma Mun sanya shi shiriya ga Banĩ Isrã'ila, cẽwa kada ku riƙi wani wakĩli baici Na.

Explanation & meanings · 1
  1. Tsakãnin Bãwan Allah Muhammadu da Mũsã, kuma an aiko Mũsã ga Banĩ Isrã'ila kawai, kuma Nũhu an ce masa bãwa amma ba a jingina shi kamar yadda aka jingina bawanSa ba. Sa'an nan kuma Jingina Yahũdu ga Nũhu ya daidaita su da sauran mutãne wajen da'awar ɗaukaka da nasaba.

ذُرِّيَّةَ مَنۡ حَمَلۡنَا مَعَ نُوحٍۚ إِنَّهُۥ كَانَ عَبۡدٗا شَكُورٗا

Zuriyar waɗanda Muka ɗauka tãre da Nũhu. Lalle ne shi ya kasance wani bãwa mai gõdiya.

وَقَضَيۡنَآ إِلَىٰ بَنِيٓ إِسۡرَٰٓءِيلَ فِي ٱلۡكِتَٰبِ لَتُفۡسِدُنَّ فِي ٱلۡأَرۡضِ مَرَّتَيۡنِ وَلَتَعۡلُنَّ عُلُوّٗا كَبِيرٗا

Kuma Mun hukunta zuwa ga Bani Isrã'ĩla a cikin Littãfi, cewa lalle ne, kunã yin ɓarna a cikin ƙasa sau biyu, kuma lalle ne kunã zãlunci, zãlunci mai girma.

فَإِذَا جَآءَ وَعۡدُ أُولَىٰهُمَا بَعَثۡنَا عَلَيۡكُمۡ عِبَادٗا لَّنَآ أُوْلِي بَأۡسٖ شَدِيدٖ فَجَاسُواْ خِلَٰلَ ٱلدِّيَارِۚ وَكَانَ وَعۡدٗا مَّفۡعُولٗا

To idan wa'adin na farkonsu yajẽ, za Mu aika, a kanku waɗansu bãyi Nãmu, ma'abũta yãƙi mafĩ tsanani, har su yi yãwo a tsakãnin gidãjenku, kuma yã zama wa'adi abin aikatawa.

Explanation & meanings · 1
  1. Sun yi fasãdi da barin aiki da Taurãti, sabõda haka aka aika Jãlũta a kansu. Ya kashe su kuma ya kãma zuriyarsu.