Skip to content
الكَهف /

Aya 21

18 : 21

Aya 21 of الكَهف (18 : 21). This page carries the verse in the Uthmani script with a translation of its meaning, at a stable URL that can be cited on its own.

الكَهف Ayoyi 110
Sura · الكَهف
Hausa · Gummi
18 : 21

وَكَذَٰلِكَ أَعۡثَرۡنَا عَلَيۡهِمۡ لِيَعۡلَمُوٓاْ أَنَّ وَعۡدَ ٱللَّهِ حَقّٞ وَأَنَّ ٱلسَّاعَةَ لَا رَيۡبَ فِيهَآ إِذۡ يَتَنَٰزَعُونَ بَيۡنَهُمۡ أَمۡرَهُمۡۖ فَقَالُواْ ٱبۡنُواْ عَلَيۡهِم بُنۡيَٰنٗاۖ رَّبُّهُمۡ أَعۡلَمُ بِهِمۡۚ قَالَ ٱلَّذِينَ غَلَبُواْ عَلَىٰٓ أَمۡرِهِمۡ لَنَتَّخِذَنَّ عَلَيۡهِم مَّسۡجِدٗا

Kuma kamar wancan ne, Muka nũna su (gare su) dõmin su san lalle wa'adin Allah gaskiya ne, kuma lalle ne Sa'a bãbu shakka a cikinta. A lõkacin da suke jãyayyar al'amarinsu a tsakãninsu sai suka ce: "Ku gina wani gini a kansu, Ubangijinsu ne Mafi sani game da su." Waɗanda suka rinjãya a kan al'amarinsu suka ce: "Lalle mu riƙi masãllãci a kansu."

Explanation & meanings · 1
  1. Muhãwarar mũminai da kãfirai, da yadda kãfirai ke zartar da al'amari bã da ambaton yardar Allah Ubangijinsu ba. Da yadda suke yin sãri-faɗi ga matsalõlin ilmi da ya kamãta a mayar da saninsu ga Allah.