Skip to content
الكَهف /

Aya 9

18 : 9
الكَهف Ayoyi 110
Sura · الكَهف
Hausa · Gummi
18 : 9

أَمۡ حَسِبۡتَ أَنَّ أَصۡحَٰبَ ٱلۡكَهۡفِ وَٱلرَّقِيمِ كَانُواْ مِنۡ ءَايَٰتِنَا عَجَبًا

Ko kuwa kã yi zaton cẽwa ma'abũta kõgo da allo sun kasance abin mãmãki daga ãyõyin Allah?

Explanation & meanings · 1
  1. Lõkacin da Allah Ya ce: "kada Annabi ya wahalar da kansa dõmin baƙin cikin ba a karɓi maganarsa ba, sai Ya ba shi lãbãrin ma'abũta kõgo, yadda suka yi gudun hijira da addininsu, Allah Ya tsare su daga wahala, a cikin halin abin al'ajabi. Sa'an nan ƙissar ta tattara a kan ladubba waɗanda ake nħman Mutum ya tsare su tãre da Ubangijinsa a cikin dukan mõtsinsa, kamar yadda bayãni zai nũna.