Skip to content
Al'kahf /

Aya 76

18 : 76

Aya 76 of Al'kahf (18 : 76). This page carries the verse in the Uthmani script with a translation of its meaning, at a stable URL that can be cited on its own.

Al'kahf Ayoyi 110
Sura · Al'kahf
Hausa · Gummi
18 : 76

قَالَ إِن سَأَلۡتُكَ عَن شَيۡءِۭ بَعۡدَهَا فَلَا تُصَٰحِبۡنِيۖ قَدۡ بَلَغۡتَ مِن لَّدُنِّي عُذۡرٗا

Ya ce: "Idan na tambaye ka daga wani abu a bãyanta, to, kada ka abũce ni. Lalle ne, kã isa ga iyakar uzuri daga gare ni."

Explanation & meanings · 1
  1. Mũsã ya kãsa yin haƙuri a bãyan ya yi alkawura cewa zai yi haƙuri, sabõda ba yã halatta ga mutum ya ga abin da ya sãɓa wa shari'a, sa'an nan ya yi shiru. Dã zai halatta a yi shiru, dã Mũsã bai yi magana ba ga aikin mãlamin da Allah Ya umurce shi da ya tafi ya karɓo ilmi daga gare shi, a bãyan Yã gaya masa cewa,Yã bã shi wani ilmi daga gare shi. Dõmin sharaɗin da ya sãɓa wa shari'a warwararre ne. Sabõda haka Allah bai zargi Mũsa ba a bayan sun rabu. Sake al-munkar wãjibi ne a cikin ladubban shari'a gwargwadon hãli, kamar yadda yake a cikin Hadĩsi. Ana gabãtar da hukuncin da ya fi tsanani.