18 : 59
وَتِلۡكَ ٱلۡقُرَىٰٓ أَهۡلَكۡنَٰهُمۡ لَمَّا ظَلَمُواْ وَجَعَلۡنَا لِمَهۡلِكِهِم مَّوۡعِدٗا
Kuma waɗancan alƙaryu Mun halaka su, a lõkacin da suka yi zãlunci, kuma Muka sanya lõkacin alkawarin, ga halaka su.
Explanation & meanings · 2
- Alƙaryun Ãdãwa da samũdãwa da waɗansunsu.
- Kõme Allah Zai yi, sai Yã sanya masa lõkacin aukuwarsa, kuma bã zai aukun ba sai ajalin nan da Ya ambata masa ya zo.