Skip to content
الكَهف /

Aya 42

18 : 42

Aya 42 of الكَهف (18 : 42). This page carries the verse in the Uthmani script with a translation of its meaning, at a stable URL that can be cited on its own.

الكَهف Ayoyi 110
Sura · الكَهف
Hausa · Gummi
18 : 42

وَأُحِيطَ بِثَمَرِهِۦ فَأَصۡبَحَ يُقَلِّبُ كَفَّيۡهِ عَلَىٰ مَآ أَنفَقَ فِيهَا وَهِيَ خَاوِيَةٌ عَلَىٰ عُرُوشِهَا وَيَقُولُ يَٰلَيۡتَنِي لَمۡ أُشۡرِكۡ بِرَبِّيٓ أَحَدٗا

Kuma aka halaka dukan 'ya'yan itãcensa, sai ya wãyi gari yanã jũyar da tãfunansa biyu, sabõda abin da ya kashe a cikinta, alhãli kuwa ita tanã kwance a kan rassanta, kuma yanã cẽwa, "Kaitõna, dã dai ban tãra wani da Ubangijina ba!"

Explanation & meanings · 1
  1. Ya yi nadãmar halakar gõnar kawai, amma bai yi nadãmar kãfircin shirkin da ya yi ba, sabõda haka Allah bai mayar masa da badalinta ba. Daga nan kuma anã fahimtar cewa rashin mai da al'amari ga Allah shirku ne, kuma girman kai sabõda dũkiya, shirku ne wanda ƙawar dũniya ke sanya wãwãye a ciki.