Skip to content
Al'kahf /

Aya 109

18 : 109

Aya 109 of Al'kahf (18 : 109). This page carries the verse in the Uthmani script with a translation of its meaning, at a stable URL that can be cited on its own.

Al'kahf Ayoyi 110
Sura · Al'kahf
Hausa · Gummi
18 : 109

قُل لَّوۡ كَانَ ٱلۡبَحۡرُ مِدَادٗا لِّكَلِمَٰتِ رَبِّي لَنَفِدَ ٱلۡبَحۡرُ قَبۡلَ أَن تَنفَدَ كَلِمَٰتُ رَبِّي وَلَوۡ جِئۡنَا بِمِثۡلِهِۦ مَدَدٗا

Ka ce: "Dã tẽku ta kasance tawada ga (rubũtun) kalmõmin Ubangijina, lalle ne dã tẽkun ta ƙãre a gabãnin kalmõmin Ubangijĩna su ƙãre, kuma kõda mun jẽ da misãlinsa dõmin ƙari."

Explanation & meanings · 1
  1. Ma'anar ãyar nan ita ce Allah ne Mafi sani. llmin Allah bã shi da iyãka, kõ kalmõmin da suka ɗauki ma'anõninsa, bã zã a iya rubuta su ba, balle ma'anõnin da ke cikinsu. Sabõda haka abin da ke hankali a mutum, shĩ ne ya yi aiki da ɗan ilmin da Allah Ya umurce shi da aiki dashi. Idan ya nemi ya wuce nan, to, ya halakar da kansa dõmin bai san inda zai fãɗa ba. Wannan ilmin shi ne sharĩ'a da aiki da ita.