18 : 54
وَلَقَدۡ صَرَّفۡنَا فِي هَٰذَا ٱلۡقُرۡءَانِ لِلنَّاسِ مِن كُلِّ مَثَلٖۚ وَكَانَ ٱلۡإِنسَٰنُ أَكۡثَرَ شَيۡءٖ جَدَلٗا
Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun jujjũya, a cikin wannan Alƙur'ãni, daga kõwane irin misãli ga mutãne (dõmin su gãne, su bi sharĩ'a), kuma mutum yã kasance mafi yawan abu ga jidãli.
Explanation & meanings · 1
- Jidãli, shĩ ne jãyayya, alhãli kuwa mutum yã san yanã kan ƙarya.