Skip to content
الكَهف /

Aya 65

18 : 65
الكَهف Ayoyi 110
Sura · الكَهف
Hausa · Gummi
18 : 65

فَوَجَدَا عَبۡدٗا مِّنۡ عِبَادِنَآ ءَاتَيۡنَٰهُ رَحۡمَةٗ مِّنۡ عِندِنَا وَعَلَّمۡنَٰهُ مِن لَّدُنَّا عِلۡمٗا

Sai suka sãmi wani bãwa daga bãyin Mu, Mun bã shi wata rahama daga wurin Mu, kuma Mun sanar da shi wani ilmi daga gun Mu.

Explanation & meanings · 1
  1. Rahama a nan ita ce Annabci sabõda cħwa kuma an bã shi ilmi daga gun Allah, kuma ya yi hukunci da shi. Ilmin ilhãma bã a yin hukunci da shi dõmin Annabãwa kawai Allah Ya tsare daga kuskure game da wahayi. Wannan ne bambanci bayyananne a tsakanin wahayin Annabci da wahayin walicci. Haka mu'ijiza da karãma, su duka sãɓãwar al'ada ne, amma mu'ujizar Annabi an san zã ta zo daga bãkin wanda aka yi dõminsa, amma karãma bãbu mai saninta, sai tã auku. Sabõda waliyyi bã ya iya yin tãkara, amma annabi yana iya yin tãkara a kan maƙiyansa.