Menene hukuncin mace idan ta yi haila bayan shigar lokacin sallah? Shin yana wajaba a kanta sai ta rama idan ta samu tsarki? haka nan idan ta samu tsarki kafin fitar lokacin sallar?
السؤال
TAMBAYA TA 1:
Menene hukuncin mace idan ta yi haila bayan shigar lokacin sallah? Shin yana wajaba a kanta sai ta rama idan ta samu tsarki? haka nan idan ta samu tsarki kafin fitar lokacin sallar?
س31: ما الحكم إذا حاضت المرأة بعد دخول وقت الصلاة؟ وهل يجب عليها أن تقضيها إذا طهرت؟ وكذلك إذا طهرت قبل خروج وقت الصلاة؟
الجواب
AMSA TA 1:
Na farko: idan mace ta yi haila bayan shigar lokaci watoi: Bayan shigar lokacin sallah- to, yana wajaba a kanta idan ta yi tsarki ta rama wannan sallar da ta yi haila a cikin lokacinta, idan ba ta yi sallar ba kafin hailar ta zo mata.
Hakan kuwa sabo da faɗar Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -:
"Wanda ya riski raka'a ɗaya daga cikin sallah, to, hakiƙa ya riski sallah".
Idan gwargwadon samun raka'a ɗaya ne mace ta riska, sai kuma haila ta zo mata kafin ta yi sallah, to, idan ta yi tsarki ramuwa ta lazimce ta.
Na biyu: Idan ta yi tsarkin haila kafin fitar lokacin sallah, to, ramuwar wannan sallar tana wajaba a kanta, da kuma za ta sami tsarki kafin rana ta ɓullo da misalin raka'a, to, ya wajaba a kanta ta rama sallar Asuba.
Da za ta sami tsarki, kafin faɗuwar rana da gwargwadon raka'a ɗaya, da sallar La'asar ta wajaba a kanta,
Da za ta sami tsarki kafin tsakiyar dare da kimanin raka'a ɗaya, da ramuwar sallar Isha'i ta wajaba a kanta,
Idan ta sami tsarki bayan tsakiyar dare, to, ba ya wajaba a kanta ta rama sallar Isha'i, kuma yana wajaba a kanta ta sallaci sallar Asuba, idan lokacinta ya zo,
Allah - maɗaukakin Sarki - Ya ce: {Idan kun nutsu sai ku tsayar da sallah, haƙiƙa sallah ta kasance farilla mai lokaci a kan muminai} [Al-Nisa'i: 103],
Ai: Farilla ce mai lokaci iyakantacce, ba ya halatta ga mutum ya fitar da sallah daga lokacinta, ko kuma fara yin ta kafin lokacinta.
ﺟ31: أولًا: المرأة إذا حاضت بعد دخول الوقت -أي: بعد دخول وقت الصلاة- فإنه يجب عليها إذا طهرت أن تقضي تلك الصلاة الّتي حاضت في وقتها، إذا لم تصلّها قبل أن يأتيها الحيض،
وذلك لقول الرسول ﷺ:
«مَنْ أَدْرَكَ رَكْعَةً مِنَ الصَّلَاةِ فَقَدْ أَدْرَكَ الصَّلَاةَ» [1]،
فإذا أدركت المرأة من وقت الصلاة مقدار ركعةٍ، ثم حاضت قبل أن تصلّي، فإنها إذا طهرت يلزمها القضاء.
[11] تقدم تخريجه.
ثانيًا: إذا طهرت من الحيض قبل خروج وقت الصلاة فإنه يجب عليها قضاء تلك الصلاة، فلو طهرت قبل أن تطلع الشمس بمقدار ركعةٍ وجب عليها قضاء صلاة الفجر،
ولو طهرت قبل غروب الشمس بمقدار ركعةٍ وجبت عليها صلاة العصر،
ولو طهرت قبل منتصف الليل بمقدار ركعةٍ وجب عليها قضاء صلاة العشاء،
فإن طهرت بعد منتصف الليل لم يجب عليها صلاة العشاء، وعليها أن تصلّي الفجر إذا جاء وقتها، قال الله سبحانه وتعالى:
﴿...فَإِذَا ٱطۡمَأۡنَنتُمۡ فَأَقِيمُواْ ٱلصَّلَوٰةَۚ إِنَّ ٱلصَّلَوٰةَ كَانَتۡ عَلَى ٱلۡمُؤۡمِنِينَ كِتَٰبٗا مَّوۡقُوتٗا﴾
[النساء:103]،
أي: فرضًا مؤقتًا بوقتٍ محدودٍ، لا يجوز للإنسان أن يخرج الصلاة عن وقتها، ولا أن يبدأ بها قبل وقتها.