Na je aikin hajji, sai al'ada ta wata-wata ta zo min, sai na ji kunyar in faɗawa kowa, na shiga cikin Harami, na yi sallah, na yi ɗawafi, na yi sa'ayi, menene ya wajaba a kaina, tare da sanin cewa ta zo min ne bayan biƙi?
السؤال
TAMBAYA TA 1:
Na je aikin hajji, sai al'ada ta wata-wata ta zo min, sai na ji kunyar in faɗawa kowa, na shiga cikin Harami, na yi sallah, na yi ɗawafi, na yi sa'ayi, menene ya wajaba a kaina, tare da sanin cewa ta zo min ne bayan biƙi?
س57: حججت، وجاءتني الدورة الشهرية، فاستحييت أن أخبر أحدًا، ودخلت الحرم، فصليت، وطفت، وسعيت، فماذا علي، علمًا بأنها جاءت بعد النّفاس؟
الجواب
AMSA TA 1:
Ba ya halatta ga mace idan ta kasance tana haila ko biƙi ta yi sallah, ko a Makka ko a garinta ko ma a kowane waje ne;
Sabo da faɗin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - game da mace: "Shin idan tana haila ba ba ta yin sallah da azumi ba?"
Haƙiƙa Musulmai sun haɗu a kan cewa, ba ya halatta ga wata mai haila ta yi azumi, kuma ba ya halatta ta yi sallah.
Yana wajaba a kan wannan matar da ta aikata hakan ta tuba zuwa ga Allah, ta nemi gafarar bin da tya afku gareta.
Amma ɗawafin da ta yi a yanayin haila, to, ba ingantacce ba ne, amma sa'ayinta shi ingantacce ne; sabo da magana mafi rinjaye ita ce halaccin gabatar da sa'ayi a kan ɗawafi a hajji, a bisa wannan yana wajaba a kanta ta sake ɗawafin; sabo da ɗawafin Ifada rukuni ne daga rukunan hajji, fita daga harama ta biyu ba ta cika sai da shi.
Gini a bisa haka, haƙiƙa wannan matar mijinta ba zai yi mu'amalar aure da ita ba- in tana da miji - har sai ta yi ɗawafi, ba za'a ɗaura mata aure ba -in ta kasance mara aure- har sai ta yi ɗawafi, Allah maɗaukakin sarki Shi ne Masani.
ﺟ57: لا يحلّ للمرأة إذا كانت حائضًا أو نفساء أن تصلّي، سواء في مكة أو في بلدها أو في أيّ مكانٍ؛ لقول النبيّ ﷺ في المرأة:
«أَلَيْسَ إِذَا حَاضَتْ لَمْ تُصَلِّ، وَلَمْ تَصُمْ؟» [1]،
وقد أجمع المسلمون على أنه لا يحلّ لحائضٍ أن تصوم، ولا يحلّ لها أن تصلّي.
[28] تقدم تخريجه.
وعلى هذه المرأة التي فعلت ذلك، عليها أن تتوب إلى الله، وأن تستغفر ممّا وقع منها.
وأما طوافها حال الحيض فهو غير صحيحٍ، وأما سعيها فصحيحٌ؛ لأن القول الراجح جواز تقديم السعي على الطواف في الحجّ، وعلى هذا فيجب عليها أن تعيد الطواف؛ لأن طواف الإفاضة ركنٌ من أركان الحجّ، ولا يتمّ التحلّل الثاني إلا به.
وبناءً عليه فإن هذه المرأة لا يباشرها زوجها -إن كانت متزوّجةً- حتى تطوف، ولا يعقد عليها النّكاح -إن كانت غير متزوّجةٍ- حتى تطوف، والله تعالى أعلم.