Idan mai haila ko mai biƙi ta sami tsarki a lokacin la'asar, shin sallar azahar ta lazimceta tare da la'asar, ko kuma la'asar ce kawai ta lazimce ta?
السؤال
TAMBAYA TA 1:
Idan mai haila ko mai biƙi ta sami tsarki a lokacin la'asar, shin sallar azahar ta lazimceta tare da la'asar, ko kuma la'asar ce kawai ta lazimce ta?
س12: إذا طهرت الحائض أو النّفساء وقت العصر، فهل تلزمها صلاة الظّهر مع العصر، أو لا يلزمها سوى العصر فقط؟
الجواب
AMSA TA 1:
Magana mai rinjaye, a wannan mas'ala,: ba abin da ya lazimce ta, sai la'asar kawai; sabo da babu dalili a kan wajibcin sallar azahar, kuma asali shi ne kuɓutar kai (rashin wajibcin), sannan kuma Annabi - tsira da amincin allah su tabbata a gare shi - ya ce:
"Wanda ya riski raka'a kafin rana ta faɗi, to, haƙiƙa ya riski la'asar",
Bai ambaci cewa ya riski azahar ba, da a ce azahar wajibi ce da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya bayyana shi, kuma sabo da mace da za ta yi haila, bayan shigar lokacin azahar, ba abin da zai lazimceta sai ramuwar sallar azahar banda la'asar, tare da cewa ana haɗa azahar da la'asar, babu banbanci tsakaninta da yanayin da ya zo a tambayar.
A bisa wannan, magana mafi rinjaye, za ta kasance cewa ba abin da ya lazimceta sai sallar la'asar kawai, saboda abin da nassi da Ƙiyasi suka nuna, haka nan sha'anin ya ke da za ta sami tsarki kafin fitar lokacin sallar Isha'i, babu abinda yake lazimtarta sai sallar isha'i, kuma sallar magariba ba ta lazimceta ba.
ﺟ12: القول الراجح في هذه المسألة: أنه لا يلزمها إلا العصر فقط؛ لأنه لا دليل على وجوب صلاة الظّهر، والأصل براءة الذّمة، ثم إن النبي ﷺ قال:
«مَنْ أَدْرَكَ رَكْعَةً مِنَ الْعَصْرِ قَبْلَ أَنْ تَغْرُبَ الشَّمْسُ فَقَدْ أَدْرَكَ الْعَصْرَ» [1]،
ولم يذكر أنه أدرك الظّهر، ولو كان الظّهر واجبًا لبينه النبيّ ﷺ، ولأن المرأة لو حاضت بعد دخول وقت الظّهر لم يلزمها إلا قضاء صلاة الظّهر دون صلاة العصر، مع أن الظّهر تجمع إلى العصر، ولا فرق بينها وبين الصّورة التي وقع السّؤال عنها.
[2] البخاري، كتاب الصوم، باب الحائض تترك الصوم والصلاة (1951).
وعلى هذا يكون القول الراجح أنه لا يلزمها إلا صلاة العصر فقط؛ لدلالة النصّ والقياس عليها، وكذلك الشأن فيما لو طهرت قبل خروج وقت العشاء، فإنه لا يلزمها إلا صلاة العشاء، ولا تلزمها صلاة المغرب.