Wasu mata da suke zubar da ciki, yanayin su ba ya wuce: ko dai mace ta zubar da cikin kafin halittar jaririn ta cika, ko kuma ta zubar bayan halittar sa da bayyanar tsarin sa, menene hukuncin azuminta a wannan ranar da ta zubar da cikin a cikin sa, da azumin kwanakin da ta ga jini a cikin su?
السؤال
TAMBAYA TA 1:

س13: بعض النّساء اللاتي يجهضن لا يخلو الحال: إمّا أن تجهض المرأة قبل تخلّق الجنين، وإما أن تجهض بعد تخلّقه وظهور التخطيط فيه، فما حكم صيامها ذلك اليوم الذي أجهضت فيه، وصيام الأيام الّتي ترى فيها الدم؟
الجواب
AMSA TA 1:
Idan ɗan tayin halittar sa ba ta cika ba, to, haƙiƙa wannan jinin nata ba jinin biƙi ba ne, a bisa haka za ta yi azumi, za ta yi sallah, kuma azuminta ingantacce ne.
Idan kuma ɗan tayin an kammala halittar sa,to haƙiƙa jinin, jinin biƙi ne, ba ya halatta a gareta ta yi sallah a cikin sa, ko kuma ta yi azumi.
Ƙa'ida a wannan mas'alar ko abin da zai kiyaye mana ita: Shi ne cewa idan ɗan tayi an kammala halittar sa, to, jinin, jinin biƙi ne, idan kuma ba'a kammala hailittar ba, to, ba jinin biƙi ba ne, Idan jinin ya kasance jinin biƙi, to, abin da ya haramta a kan mai biƙi ya haramta a kanta, idan kuma ya kasance ba jinin biƙi bane, to, hakan bai haramta a kanta ba.
ﺟ13: إذا كان الجنين لم يخلّق فإن دمها هذا ليس دم نفاسٍ، وعلى هذا فإنها تصوم وتصلّي، وصيامها صحيحٌ.
وإذا كان الجنين قد خلّق فإن الدم دم نفاسٍ، لا يحلّ لها أن تصلّي فيه، ولا أن تصوم.
والقاعدة في هذه المسألة أو الضابط فيها: أنه إذا كان الجنين قد خلّق فالدم دم نفاسٍ، وإذا لم يخلق فليس الدم دم نفاسٍ، وإذا كان الدم دم نفاسٍ فإنه يحرم عليها ما يحرم على النّفساء، وإذا كان غير دم النّفاس فإنه لا يحرم عليها ذلك.