Skip to content

السؤال

TAMBAYA TA 1:

Fotiwar jini daga mai ciki a yinin Ramadan, shin zai yi tasiri a kan azuminta?

س14: نزول الدم من الحامل في نهار رمضان، هل يؤثّر على صومها؟

الجواب

AMSA TA 1:

Idan jinin haila ya fito, alhalin mace tana azumi, to, azuminta ya ɓaci; sabo da faɗin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -:

"Shin idan tana haila ba ba ta yin sallah da azumi ba?".

Da wannan ne ya sa mu ke lissafa shi daga cikin masu karya azumi, biƙi shi ma irinsa ne, fitar jinin haila da biƙi masu ɓata azumi ne.

Fitar jini daga mai ciki a yinin Ramadan, idan ya kasance haila ne, to, shi kamar hailar mara ciki ce, ai zai yi tasiri a azuminta, idan kuma ba haila ba ne, to ba zai yi tasiri ba.

Hailar da za ta iya zuwa daga mai ciki, ita ce hailar da ta zamo ɗoɗar ba ta ɗauke ba tun da aka samu cikin, a'a ta kasance yana zuwammata a lokutantan da aka saba da su, wannan haila ce a bisa magana mafi rinjaye, hukunce-hukuncen haila sun tabbata a game da shi.

Amma idan jinin ya ɗauke mata, sannan kuma daga baya ta zamo tana ganin jinin, amma ba shi ne jinin da ta saba ba, to, wannan ba ya tasiri a kan azuminta; sabo da ba haila ba ne.

ﺟ14: إذا خرج دم الحيض والأنثى صائمةٌ فإن صومها يفسد؛ لقول النبيّ ﷺ:

«أَلَيْسَ إِذَا حَاضَتْ لَمْ تُصَلِّ، وَلَمْ تَصُمْ؟» [1]

ولهذا نعدّه من المفطّرات، والنّفاس مثله، وخروج دم الحيض والنّفاس مفسدٌ للصوم.

[3] البخاري، كتاب الصوم، باب الحائض تترك الصوم والصلاة (1951).

ونزول الدم من الحامل في نهار رمضان إذا كان حيضًا فإنه كحيض غير الحامل، أي: يؤثّر على صومها، وإن لم يكن حيضًا فإنه لا يؤثّر.

والحيض الّذي يمكن أن يقع من الحامل هو أن يكون حيضًا مطردًا لم ينقطع عنها منذ حملت، بل كان يأتيها في أوقاتها المعتادة، فهذا حيضٌ على القول الراجح، يثبت له أحكام الحيض.

أما إذا انقطع الدم عنها، ثم صارت بعد ذلك ترى دمًا ليس هو الدم المعتاد، فإن هذا لا يؤثّر على صيامها؛ لأنه ليس بحيضٍ.