Skip to content

السؤال

TAMBAYA TA 1:

Shin mai haila da mai biƙi za su ci, za su sha, a yinin Ramadan?

س11: الحائض والنّفساء هل تأكلان وتشربان في نهار رمضان؟

الجواب

AMSA TA 1:

Eh, za su ci, za su sha, a yinin Ramadan, sai dai abin da ya fi hakan ya kasance a ɓoye, idan akwai wasu a tare da ita, daga cikin yara a gidan; sabo da hakan zai kawo rikitarwa a wajen su.

ج11: نعم، تأكلان وتشربان في نهار رمضان، لكن الأولى أن يكون ذلك سرًّا إذا كان عندها أحدٌ من الصّبيان في البيت؛ لأن ذلك يوجب إشكالًا عندهم.