Skip to content

Idan mai haila ko biƙi ta sami tsarki kafin alfijir, ba ta yi wanka ba, sai bayan alfijir, shin azumin ta ya inganta, ko a'a?

السؤال

TAMBAYA TA 1:

Idan mai haila ko biƙi ta sami tsarki kafin alfijir, ba ta yi wanka ba, sai bayan alfijir, shin azumin ta ya inganta, ko a'a?

س7: إذا طهرت الحائض أو النّفساء قبل الفجر، ولم تغتسل إلا بعد الفجر، فهل يصحّ صومها، أو لا؟

الجواب

AMSA TA 1:

Eh, azumin mai haila yana inganta, idan ta yi tsarki kafin alfijir, kuma ba ta yi wanka ba sai bayan ɓullowar alfijir, haka ma mai biƙi; sabo da ita a wannan lokacin tana cikin ma'abota azumi, ta yi kama da wanda ya ke da janaba, idan alfijir ya keto alhali yana da janaba, to, azumin sa ya inganta;

Sabo da faɗinSa - maɗaukakin sarki -: {To, yanzu ku rungume su kuma ku nẽmi abin da Allah yã rubũta muku. Kuma ku ci kuma ku sha har sĩlĩli fari ya bayyana a gare ku daga sĩlĩli baƙi daga alfijiri} [Al-Baƙarah: 187],

Tunda Allah - maɗaukakin sarki - Ya yi izini da yin jima'i har alfijir ya bayyana, hakan ya lazimci cewa wankan ba zai kasance ba sai bayan ɓullowar alfijir, kuma sabo da hadisin A'isha - Allah Ya yarda da ita - cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya kasance yana wayar gari da janaba sabo da jima'i da iyalinsa alhali yana azumi.

Wato: Cewa shi (Annabi) tsira da amincin a gareshi, ba ya wankan janaba sai bayan ɓullowar alfijir.

ﺟ7: نعم، يصحّ صوم المرأة الحائض إذا طهرت قبل الفجر، ولم تغتسل إلا بعد طلوع الفجر، وكذلك النّفساء؛ لأنها حينئذٍ من أهل الصوم، وهي شبيهةٌ بمن عليه جنابةٌ، إذا طلع الفجر وهو جنبٌ فإن صومه يصحّ؛ لقوله تعالى:

﴿...فَٱلۡـَٰٔنَ بَٰشِرُوهُنَّ وَٱبۡتَغُواْ مَا كَتَبَ ٱللَّهُ لَكُمۡۚ وَكُلُواْ وَٱشۡرَبُواْ حَتَّىٰ يَتَبَيَّنَ لَكُمُ ٱلۡخَيۡطُ ٱلۡأَبۡيَضُ مِنَ ٱلۡخَيۡطِ ٱلۡأَسۡوَدِ مِنَ ٱلۡفَجۡرِ...﴾

[البقرة:187]،

وإذا أذن الله تعالى بالجماع إلى أن يتبين الفجر لزم من ذلك ألّا يكون الاغتسال إلا بعد طلوع الفجر، ولحديث عائشة رضي الله عنها

«أَنَّ النَّبِيَّ ﷺ كَانَ يُصْبِحُ جُنُبًا مِنْ جِمَاعِ أَهْلِهِ وَهُوَ صَائِمٌ» [1].

أي: أنه عليه الصلاة والسلام لا يغتسل عن الجنابة إلا بعد طلوع الصّبح.

[1] البخاري، كتاب الصوم، باب اغتسال الصائم (1931)، ومسلم، كتاب الصوم، باب صحة صوم من طلع عليه الفجر وهو جنب (75) (1109).