Idan mace ta ji alamun (fitar) jini, bai fito ba kafin faɗuwar rana, ko kuma ta ji raɗaɗin al'ada, shin azuminta na wannan yinin ya inganta, ko kuma yana wajaba a kanta ta rama shi?
السؤال
TAMBAYA TA 1:
Idan mace ta ji alamun (fitar) jini, bai fito ba kafin faɗuwar rana, ko kuma ta ji raɗaɗin al'ada, shin azuminta na wannan yinin ya inganta, ko kuma yana wajaba a kanta ta rama shi?
س8: إذا أحست المرأة بالدم، ولم يخرج قبل الغروب، أو أحست بألم العادة، فهل يصحّ صيامها ذلك اليوم، أو يجب عليها قضاؤه؟
الجواب
AMSA TA 1:
Idan mace mai tsarki ta ji alamun tahowar haila alhali tana azumi, sai dai bai fito ba sai bayan faɗuwar rana, ko ta ji ciwon haila, sai dai bai fito ba sai bayan faɗuwar rana, to, azumin wannan ranar ingantacce ne, ba ya wajaba a kanta ta sake shi, idan na farilla ne, kuma ladanta bai ɓaci ba idan na nafila ne.
ﺟ8: إذا أحست المرأة الطاهرة بانتقال الحيض وهي صائمةٌ، ولكنه لم يخرج إلا بعد غروب الشمس، أو أحست بألم الحيض، ولكنه لم يخرج إلا بعد غروب الشمس، فإن صومها ذلك اليوم صحيحٌ، وليس عليها إعادته إذا كان فرضًا، ولا يبطل الثواب به إذا كان نفلًا.