Skip to content

Idan ɗigon jini kaɗan ya saukowa mace a wunin Ramadan, kuma wannan jinin ya zarce mata tsawon Ramadan, alhalin tana azumin, shin azuminta ingantacce ne?

السؤال

TAMBAYA TA 1:

Idan ɗigon jini kaɗan ya saukowa mace a wunin Ramadan, kuma wannan jinin ya zarce mata tsawon Ramadan, alhalin tana azumin, shin azuminta ingantacce ne?

س6: إذا نزل من المرأة في نهار رمضان نقط دمٍ يسيرةٌ، واستمر معها هذا الدم طوال شهر رمضان وهي تصوم، فهل صومها صحيحٌ؟

الجواب

AMSA TA 1:

Eh, azuminta ingantacce ne, amma wannan ɗige-ɗigen jinin ba komai ba ne; sabo da daga jijiyoyi ya ke, kuma an ruwaito daga Aliyyu ɗan Abu Ɗalib - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Lallai waɗannan ɗige-ɗigen waɗanda suka zamo tamkar haɓo ne na hanci, ba haila bane, haka ake ambata daga gareshi, Allah Ya yarda da shi.

ﺟ6: نعم، صومها صحيحٌ، وأما هذه النّقط فليست بشيءٍ؛ لأنها من العروق، وقد أثر عن عليّ بن أبي طالبٍ رضي الله عنه أنه قال: إن هذه النّقط التي تكون كرعاف الأنف ليست بحيضٍ، هكذا يذكر عنه رضي الله عنه.