Shin mace mai biƙi, za ta zauna kwana arba'in ba ta sallah, ba ta azumi, ko kuwa za ta yi lura ne da yankewar jinin, duk lokacin da ya yanke za ta yi tsarki ta yi salla? kuma menene mafi ƙarancin lokacin tsarki?
السؤال
TAMBAYA TA 1:
Shin mace mai biƙi, za ta zauna kwana arba'in ba ta sallah, ba ta azumi, ko kuwa za ta yi lura ne da yankewar jinin, duk lokacin da ya yanke za ta yi tsarki ta yi salla? kuma menene mafi ƙarancin lokacin tsarki?
س5: المرأة النّفساء هل تجلس أربعين يومًا لا تصلّي ولا تصوم، أو العبرة بانقطاع الدم عنها، فمتى انقطع تطهرت وصلت؟ وما أقلّ مدةٍ للطّهر؟
الجواب
AMSA TA 1:
Mai biƙi ba ta da wani lokaci iyakantacce, kawai a duk lokacin da jini ya zo za ta zauna, ba za ta yi sallah ba, ba za ta yi azumi ba, mijinta ba zai sadu da ita ba.
Idan ta ga tsarki -ko da kafin kwana arba'in ne, ko da kwana goma kawai ta zauna ko biyar- to, za ta yi sallah, za ta yi azumi, mijinta zai sadu da ita, babu wani laifi a yin haka.
Abu mai muhimmanci shi ne cewa biƙi lamari ne da ake iya gani, hukunce-hukunce suna ratayuwa ne da samuwar sa ko rashin sa, duk lokacin da ya kasance samamme, to, hukunce-hukuncen sa sun tabbata, duk kuma lokacin da ta samu tsarki, to, ta wofinta daga hukunce-hukuncen sa.
Sai dai da zai ƙaru a kan kwana sittin, to, shi kenan ta zama mai istihala (jinin rashin lafiya), za ta zauna gwargwadon abin da ya dace da hailarta kawai, sannan sai ta yi wanka, ta yi sallah.
ﺟ5: النّفساء ليس لها وقتٌ محدودٌ، بل متى كان الدم موجودًا جلست، ولم تصلّ، ولم تصم، ولم يجامعها زوجها.
وإذا رأت الطّهر -ولو قبل الأربعين، ولو لم تجلس إلا عشرة أيامٍ أو خمسة أيامٍ- فإنها تصلّي، وتصوم، ويجامعها زوجها، ولا حرج في ذلك.
والمهمّ أن النّفاس أمرٌ محسوسٌ، تتعلق الأحكام بوجوده أو عدمه، فمتى كان موجودًا ثبتت أحكامه، ومتى تطهرت منه تخلت من أحكامه.
لكن لو زاد على السّتّين يومًا فإنها تكون مستحاضةً، تجلس ما وافق عادة حيضها فقط، ثم تغتسل، وتصلّي.