Skip to content

أبو حامد محمد بن محمد بن محمد الغزَّالي

الإسم

Abu Hamid, Muhammad dan Muhammad dan Muhammad Ghazali

اسم الشهرة

Abu Hamid Ghazali

نبذة مختصرة

Muhammad dan Muhammad dan Muhammad addusi, Abu Hamid Ghazzali da yi wa Zaira shadda, haka Ibnu Sam’ani ya yi wasalinsa da Ibnu Kasir da Nawawi da kuma Ibnu Khallikan da Ibnu Dakik Id da Zahabi da Subki da Sakhawi da Murtada da Zabidi, Shi ne abinda ya fi karfi, dudda sabanin da yake a ciki, an haife shi a shekara ta 450, bayan hijira, masanin Usul ne malamin Fikhu BaShafi’e, yana littattafai masu yawa, daga cikinsu: Ihya’u Ulumuddin, da Almustasfa Fee Ululul Fikh, a fikihu kuma: Awajiz, da Alwasid, da Albasid, ya fada a falsafa sannan ya barta ya yi mata raddi, bayan haka kuma ya afkawa abinda ake cewa Ilmul Kalam, ya kware a Usul dinsa da Mukaddimat dinsa, sannan ya bari bayan barnar dake ciki ta bayyana a gare shi da tufka da warwarar da ke ciki da jayayyar masu shi, ya kasance mai ilmil kalam a lokacin da yake raddi ga masu Falsafa, a lokacin ne aka yi masa lakabi da Hujjatul Islam, domin ya kure su. Sannan ya kama hanyar Badiniyya (masu zahiri da badini), ya koyi iliminsu sannan ya barsu ya yi bayani munin barnar Akidun Badiniyya, da yadda suke wasa da nassoshi da Hukunce- Hukunce. Sannan ya bi Sufanci, Ibnu Sallah ya fada dangane da shi: (Abu Hamid maganganu suna da yawa akan lamarinsa, haka maganganunsa, to Amma wadannan littattafan- wato wadanda suka sabawa daidai- ba’a kallonsu, amma shi a yi shiru akansa, sai a fawwala lamarinsa ga Allah). Zahabi ya ce: Hakika mutumin ya wallafa littafi “Tahafut” yana sukar masu falsafa, ya yaye tsaraicinsu, ya yi daidai da su a wasu wuraran yana zaton hakan gaskiya ne ya yi daidai da addini, bai kasance yana da irin riwaya ba, haka kuma ba shi da kwarewa da Sunnar Annbi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, wacce take ake gabatarwa akan hankali, an kimsa masa son karanta littafin “Rasa’ilu Ikhawinis Safah” kuma (littafin mugun cuta ce, ceta ce mai wahalar sha’ani, kuma cuta ce mai kisa, da badin Abu Hamid ya kasance mai kaifin basira ba, kuma cikin zababbun masu Ilhadi ba da an rasa shi. Ya zama dole a kiyayi wadannan littattafan, ku gudu da addininku daga barin shubuhohin mutanan farko in ba haka ba zaku afka cikin rudani)). Abubakar Ibnul Arabi ya ce: ((Malamimmu Abu Hamid ya hadiyi falsafa sai ya yi kokarin amayar da ita amma bai iya ba)). Alkali Iyadh ya ce: (Malam Abu Hamid yana da muggan labaru, da littattafai abin tsoro, ya wuce iyaka a sufanci, ya tsaya tsayin daka domin taimakon harkarsu , kuma yana kira zuwa ga hakan, ya wallafa akan hakan (sufanci) littattafai masu yawa wato: “Ihya’u”, an yi tsoka a wurare a cikin littafin , saboda littafin zaton mutane da dama ya yi muni, Allah shi ne mafi sanin sirrinsa. An zartar da umarnin shugaba da fatawar malamai akan kona littafin, kuma an aikata hakan. Ibnu Jauzi ya ce: Abu Hamid ya wallafa littafin Ihya’u ya cika shi da hadisai marasa asali, bai san ba su da kyau ba, ya yi magana akan Kashfu, ya fita daga tsarin malaman Fikhu)). Ya rasu shekara ta 505, bayan hijira .

المراجع

Kari (1)
الدر الثمين في أسماء المصنفين (ص 83)، تاريخ الإسلام (11/62)، سير أعلام النبلاء (19/ 322، 335، 343)، طبقات الشافعية الكبرى (6/191)، فتح المغيث (3/ 15)، ضبط الأعلام (ص144-150)، الأعلام للزركلي (7/22).