Skip to content

أبو بكر الصديق عبد الله بن أبي قحافة عثمان بن عامر القرشي التيمي

الإسم

Sayyidina Abubakar, Abdullahi dan Abu Kuhafah Usman dan Amir bakuraishe bataime

اسم الشهرة

Abubakar Al-Siddiq- Allah ya yarda da shi-

نبذة مختصرة

(Sayyidina) Abubakar Siddik, Abdullahi dan Abu Kuhafah Usman dan Amir bakuraishe bataime, Halifan Manzon Allah -tsira da amincin Allah su tabbata a gare sh— farkon wanda ya musulunta cikin maza, kuma daya daga cikin mutane goman da aka yi wa bushara da aljanna, kuma sahabin annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi- a kogo, hakika ya sami matsayin abokantarsa a hakan, kuma hakika Allah ya saukar da AlKur’ani ana karantawa akan hakan har ranar Alkiyama. Hakika annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya auri diyarsa, kuma tabbas ya halarci dukkan yakoki tare da annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, shi ne mafi falalar wannan al’ummar bayan annabinta, ya jagoranci mutane sallah yana liman a rashin lafiyar annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, wacce ya rasu a cikinta, annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya fada dangane da shi: ((Lalle yana cikin wanda ya kyautata min a cikin mutane Abubakar, da na kasance wanda zai dauki badadi to da na dauki Abubakar badadi, saidai ‘yan uwantaka ta Musulinci da soyayyarsa)). Bukhari ne ya ruwaito, ya rasu a shekara ta 13, bayan hijira.

المراجع

Kari (1)
الطبقات الكبرى (3/126)، الاستيعاب (4/1614)، وفيات الأعيان (3/64)، الأعلام للزركلي (4/102).