Skip to content

Na zo wurin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ina son (shiga) Musulunci, sai ya umarceni da in yi wanka da ruwa da magarya

Daga Ƙais ɗan Asim - Allah Ya yarda da shi - ya ce:

Na zo wurin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ina son (shiga) Musulunci, sai ya umarceni da in yi wanka da ruwa da magarya.

أتيتُ النبيَّ صلى الله عليه وسلم أُريدُ الإسلامَ، فأَمَرَني أن أغتَسِلَ بماءٍ وسِدرٍ.

Abu Dawud da Tirmizi da Nasa'i ne Suka Rawaito shi
Ingantacce ne
Bayani

Ƙais ɗan Asim ya zo wurin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - alhali yana son ya musulunta, sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya umarce shi ya yi wanka da ruwa da (ganyan) bishiyar magarya; don kasancewa ganyanta ana amfani da shi a tsafta; don kuma abin da take da shi na ƙamshi mai daɗi.

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

Halaccin wankan kafiri a lokacin shigarsa Musulunci.

Darajar Musulunci da kulawarsa da jiki da rai gabaɗaya.

Cakuɗa ruwa da abubuwa masu tsarki ba ya fitar da shi daga tsarki.

Abubuwa na tsafta na zamani suna tsayawa a matsayin magarya, kamar sabulu da makamantansa.

Manazarta

Sunan Abi Dawud (1/ 266) (355).

Sunan Tirmizi (1/ 595) (605).

Sunanu Nasa'i (1/ 109) (188).

Kari (3)

معالم السنن (1/111).

ذخيرة العقبى (4/131).

شرح سنن أبي داود للعباد (54/ 10).