Skip to content
الأنعَام /

Aya 121

6 : 121

Aya 121 of الأنعَام (6 : 121). This page carries the verse in the Uthmani script with a translation of its meaning, at a stable URL that can be cited on its own.

الأنعَام Ayoyi 165
6 : 121

وَلَا تَأۡكُلُواْ مِمَّا لَمۡ يُذۡكَرِ ٱسۡمُ ٱللَّهِ عَلَيۡهِ وَإِنَّهُۥ لَفِسۡقٞۗ وَإِنَّ ٱلشَّيَٰطِينَ لَيُوحُونَ إِلَىٰٓ أَوۡلِيَآئِهِمۡ لِيُجَٰدِلُوكُمۡۖ وَإِنۡ أَطَعۡتُمُوهُمۡ إِنَّكُمۡ لَمُشۡرِكُونَ

Kada ku ci daga abin da ba a ambaci sũnan Allah ba a kansa. Kuma lalle ne shĩ fãsiƙanci ne. Kuma lalle ne, shaiɗãnu, haƙĩƙa, suna yin ishãra zuwa ga masõyansu, dõmin su yi jãyayya da ku. Kuma idan kuka yi musu ɗã'a, lalle ne kũ, haƙĩƙa, mãsu shirki ne.

Explanation & meanings · 1
  1. Sabõda haka bã a cin yankan majũsu. Anã cin yankan bakitãbe, babu ruwanmu da abin da yake faɗa, tun da Allah Ya halatta mana cin abincinsu alhãli kuwa Ya san sun riga sun musanya addininsu. Idan Musulmi ya bar sũnan Allah da gangan, amma bai ambaci sũnan kõwa ba, to, akwai riwãya biyu game da haka, ci kõ rashin ci. Amma idan ya haɗa sũnan Allah da na wani, to, ba zã a ci ba, dõmin yã yi ridda.