Skip to content
Jerin Surori /

النَّجم

النَّجم is chapter 53 of the Quran and has 62 verses. This page presents it in full in the Uthmani script, with a verse-by-verse translation of its meaning.

62 Ayoyi Lambar Sura 53
Je zuwa aya
Hausa · Gummi
بِسْمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحْمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ

وَٱلنَّجۡمِ إِذَا هَوَىٰ

Inã rantsuwa da taurãron, a lõkacin da ya faku.

مَا ضَلَّ صَاحِبُكُمۡ وَمَا غَوَىٰ

Ma'abũcinku bai ɓata ba, kuma bai ƙẽtare haddi ba.

وَمَا يَنطِقُ عَنِ ٱلۡهَوَىٰٓ

Kuma bã ya yin magana daga son zuciyarsa.

إِنۡ هُوَ إِلَّا وَحۡيٞ يُوحَىٰ

(Maganarsa) ba ta zamo ba, fãce wahayi ne da ake aikõwa.

عَلَّمَهُۥ شَدِيدُ ٱلۡقُوَىٰ

(Malã'ika) mai tsananin ƙarfi ya sanar da shi.

Explanation & meanings · 1
  1. Wahayin da ke zuwa ga Annabi bãbu ɓata a cikinsa dõmin Jibrilu mai kãwo shi ga Annabi, Malã'ika ne mai ƙarfi ƙwarai, wani Shaiɗãni bã ya iya taron sa dõmin ya musanya wahayin, kuma Annabi ya san shi sõsai, kuma idan ya kãwo wahayin, sai ya sauko kusa ƙwarai da Annabi, sa'an nan shi kuma Annabi ba rikitacce ba ne, yanã cikin hankalinsa.