Skip to content
Jerin Surori /

القَمَر

القَمَر is chapter 54 of the Quran and has 55 verses. This page presents it in full in the Uthmani script, with a verse-by-verse translation of its meaning.

55 Ayoyi Lambar Sura 54
Je zuwa aya
Hausa · Gummi
بِسْمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحْمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ

ٱقۡتَرَبَتِ ٱلسَّاعَةُ وَٱنشَقَّ ٱلۡقَمَرُ

Sã'a ta yi kusa, kuma wata ya tsãge.

Explanation & meanings · 1
  1. Ƙuraishãwa suka nemi Annabi ya yi addu'a dõmin wata ya tsãge wani ɓangaren nãsa ya fãɗo a ƙasã; ya yi addu'ar, watã ya tsãge, wani abu daga gare shi ya fãɗo kamar yadda suka nema.

وَإِن يَرَوۡاْ ءَايَةٗ يُعۡرِضُواْ وَيَقُولُواْ سِحۡرٞ مُّسۡتَمِرّٞ

Kuma idan sun ga wata ãyã, sai su juya baya su ce: "Sihiri ne mai dõgẽwa!"

وَكَذَّبُواْ وَٱتَّبَعُوٓاْ أَهۡوَآءَهُمۡۚ وَكُلُّ أَمۡرٖ مُّسۡتَقِرّٞ

Kuma suka ƙaryata, kuma suka bi son zũciyarsu, alhãli kuwa kõwane al'amari (wanda suke son su tũre daga Annabi) an tabbatar da shi.

وَلَقَدۡ جَآءَهُم مِّنَ ٱلۡأَنۢبَآءِ مَا فِيهِ مُزۡدَجَرٌ

Kuma lalle, abin da yake akwai tsãwatarwa a cikinsa na lãbãraiya zo musu.

حِكۡمَةُۢ بَٰلِغَةٞۖ فَمَا تُغۡنِ ٱلنُّذُرُ

Hikima cikakka! Sai dai abũbuwan gargaɗi bã su amfãni.