Skip to content

أحمد بن عبد الحليم بن عبد السلام بن تيمية

الإسم

Ahmad dan Abdulhalim dan Abdussalam dan Taimiya

اسم الشهرة

Dan Taimiya

نبذة مختصرة

Ahmad dan AbdulHalim dan Abdussalam dan Taimiya mutumin Harran, Shehul Islam, Imam ne kuma Mujtahidi kana mujaddadi, an haife shi shekara ta 661, bayan hijira, kogin ilimai ne na riwaya da kuma na nazari, aya ce a kaifin kwakwalwa da saurin fahimta, ya kasance ba ya son a ce masa Takiyyud Din, sai dai ya shahara da hakan, da kuma Shehul Islam, babban malam Ibnu Akikil Id, ya ce: dangane da shi: A lokacin da na hadu da Ibnu Taimiya na ga mutumin da yake dukkanin ilimi ga su a kan idanuwansa, yana diban wanda ya ga dama ya bar wanda ya ga dama)) Hafiz Ibnu Hajar ya ce: ((ya yi ilimi mai zurfi ya kuma kware ya sha banban ya wuce gaba ya wallafa ya karantar ya yi fatawa ya ketare sa’anninshi ya zama wani abin mamaki wurin halarto (da karatu) da kaifin kwakwalwa da yalwatuwar ilimi da riwaya da kuma na nazari da kuma sanin mazahabobin magabata da kuma ‘yan baya)). Yana da littattafai masu yawan gaske, har Imam Zahabi yana cewa: Takan yiyu littattafan sa zuwa wannan lokacin su kai takardu 4000 ko sama da haka)), daga cikinsu: Dar’u Ta’arishul Akali wannankal, da Minhajussunnna Annabawiyyah, da Alistikama, da Aljawabus Sahih liman baddala dinal Masih, da Bayanu Talbisal Jahamiyya, da Iqtidha’us Saradil Mustakim Limukhalafati As’habil Jaheem, ya rasu shekara ta 728, bayan hijira.

المراجع

Kari (1)
المعجم المختص بالمحدثين (ص: 25) معجم الشيوخ الكبير للذهبي (1/56) فوات الوفيات(1/74) ذيل التقييد (1/325) الأعلام للزركلي (1/144)