أحمد بن محمد بن حنبل الشيباني الإمام
الإسم
Ahmad bin Muhammad bin Hanbal Asshaibani, Imam
اسم الشهرة
Ahmad bin Hanbal
نبذة مختصرة
Abu Abdullah, Ahmad bin Muhammad bin Hanbal Asshaibani Imam, an haife shi shekara ta 164, bayan hijira, daya daga cikin manyan malaman Musulinci fitattu, tarihinsa yana da yawa, kuma ya shahara, Imamus Shafi’i ya fada dangane da (Imam Ahmad): Ahmd Imam ne a abubuwa takwas: Imam ne a Hadisi, Imam ne a Fikhu, Imam ne a Lugghah, Imam ne a AlKur’ani, Imam ne a talauci, Imam ne a Zuhudu, Imam ne a Tsantse ni, Imam ne a Sunnah)), yana da matsaya shararriya a lokacin fitinar halittar AlKur’ani wacce take nuni akan iliminsa da kuma hakurinsa, har aka yi masa lakabi da Imamu Ahlussunna, wato ya bayyanar da Sunnah a lokacin yaduwar bidi’a, wannan kuma ita ce ma’anar duk wanda aka yi wa lakabi da wannan cikin malaman Sunnah, sabanin jagororin bidi’a, domin su suka kirkiro ta kuma suka zo da ita (Bidi’ar), sai aka jingina Sunnah ga masu bunta domin su suka bayyanar da ita suka kuma yada ta, aka kuma jingina bidi’a ga masu ita domin su suka fito da ita suka kirkireta. Daga cikin littattafan sa: Almusnad, da Azzuhd, da Al’ashriba, da Risalatun Fil Musi’i Salatuh, da Arraddu Alaz Zanadiqah wal Jahamiyyah, da wanin haka, almajiransa sun ruwaito daga gare shi kusan mas’aloli dubu sittin, mazahabarsa a tabbace take akan Usul da kuma Furu’i, ya rasu shekara ta 241, bayan hijira.