Skip to content

Idan mace ta ga jini a wata rana lokacin al'adarta, a ranar da ta biyo kuma ba ta ganshi ba, a tsawon yini, me ya ke wajaba a kanta ta aikata?

السؤال

TAMBAYA TA 1:

Idan mace ta ga jini a wata rana lokacin al'adarta, a ranar da ta biyo kuma ba ta ganshi ba, a tsawon yini, me ya ke wajaba a kanta ta aikata?

س15: إذا رأت المرأة في زمن عادتها يومًا دمًا، والذي يليه لا ترى الدم طيلة النهار، فماذا عليها أن تفعل؟

الجواب

AMSA TA 1:

Abin da ya ke a bayyane shi ne cewa wannan tsarkin ko bushewar da ta faru a gareta ita, a ranekun hailarta, suna bin hailar ne, ba za'a ɗaukesu a matsayin wani tsarki ba, a bisa wannan sai ta bar abubuwan da aka hana mai haila gare shi.

Sashin wasu malamai suka ce: Wacce ta kasnce ta na ganin jini a wata rana, a wata rana kuma taga tsarki, to, jinin haila ne, tsarkin kuma tsarki ne har sai ya kai kwana goma sha biyar.

Idan ya kai kwana goma sha biyar, to, abin da ya biyo bayan sa jinin istihala ne (jinin cuta ne) wannan shi ne mafi shahara, a Mazhabar Imam Ahmad ɗan Hanbal - Allah Ya yi masa rahama -.

ﺟ15: الظاهر أن هذا الطّهر أو اليبوسة التي حصلت لها في أيام حيضها تابعٌ للحيض، فلا يعتبر طهرًا، وعلى هذا فتبقى ممتنعةً ممّا تمتنع منه الحائض.

وقال بعض أهل العلم: من كانت ترى يومًا دمًا، ويومًا نقاءً، فالدم حيضٌ، والنقاء طهرٌ حتى يصل إلى خمسة عشر يومًا،

فإذا وصل إلى خمسة عشر يومًا صار ما بعده دم استحاضةٍ. وهذا هو المشهور من مذهب الإمام أحمد بن حنبلٍ رحمه الله.