Skip to content

Menene hukuncin karatun Alƙur'ani ga mai haila da mai biƙi ta hanyar dubawa, ko a haddace, a yanayi na lalura, kamar ta zamo ɗaliba ko malama?

السؤال

TAMBAYA TA 1:

Menene hukuncin karatun Alƙur'ani ga mai haila da mai biƙi ta hanyar dubawa, ko a haddace, a yanayi na lalura, kamar ta zamo ɗaliba ko malama?

س17: ما حكم قراءة الحائض والنّفساء للقرآن نظرًا وحفظًا في حال الضرورة، كأن تكون طالبةً أو معلّمةً؟

الجواب

AMSA TA 1:

Babu laifi ga mai haila, ko mai biƙi, a wajen yin karatun Alƙur'ani, idan akwai wata buƙata, kamar mace mai karantarwa, ko 'yar makaranta wacce ta ke karatun wuridinta a cikin dare ko wuni.

Amma karatun - ina nufin: karatun Alƙur'ani sabo da neman lada da sakamakon tilawar - abin da ya fi shi ne, kar ta yi; sabo da yawancin malamai, ko mafi yawansu, suna ganin cewa mai haila karatun alƙur'ani ba ya halatta a gareta.

ﺟ17: لا حرج على المرأة الحائض أو النّفساء في قراءة القرآن إذا كان لحاجةٍ، كالمرأة المعلّمة، أو الدارسة الّتي تقرأ وردها في ليلٍ أو نهارٍ.

وأما القراءة -أعني: قراءة القرآن لطلب الأجر وثواب التّلاوة- فالأفضل ألا تفعل؛ لأن كثيرًا من أهل العلم أو أكثرهم يرون أن الحائض لا يحلّ لها قراءة القرآن.