Muslulunci: shi ne ka shaida babu wani abin bautawa da gaskiya sai Allah, kuma cewa (Annabi) Muhammad manzon Allah ne, ka tsai da sallah, ka ba da zakka, ka azimci Ramadan, ka ziyarci ɗakin (Allah) idan kana da ikon tafiya zuwa gareshi
Daga Umar ɗan khaɗɗab - Allah Ya yarda da shi - ya ce:
Wata rana muna zaune a wurin Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yayin da wani mutum ya ɓullo mana mai tsananin farin tufafi, mai tsananin baƙin gashi, ba’a ganin sawunsa, kuma wani daga cikinmu bai sanshi ba, har ya zauna zuwa ga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -, sai ya jingina gwiwoyinsa zuwa gwiwoyinsa, ya ɗora tafukansa a kan cinyoyinsa, sai ya ce: Ya Muhammad, ba ni labari game da musulunci, sai manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: "Muslulunci: shi ne ka shaida babu wani abin bautawa da gaskiya sai Allah, kuma cewa (Annabi) Muhammad manzon Allah ne, ka tsai da sallah, ka ba da zakka, ka azimci Ramadan, ka ziyarci ɗakin (Allah) idan kana da ikon tafiya zuwa gareshi" ya ce: ka yi gaskiya, ya ce: Sai muka yi mamakinsa, yana tambayarsa yana gasgatashi, ya ce: Ka ba ni labari game da imani, sai ya ce: "Ka ba da gaskiya da Allah, da mala'ikunsa, da littattafansa, da manzanninsa, da ranar lahira, ka ba da gaskiya da kaddara alherinta da sharrinta". Sai ya ce: ka yi gaskiya, ya ce: Ka ba ni labari game da kyautayi, ya ce: "Ka bautawa Allah kamar kai kana ganinsa, idan ka kasance ba ka ganinsa, to, shi yana ganinka" Ya ce: ka ba ni labari game da al-ƙiyama, ya ce: Wanda ake tambayar bai fi wanda yake tambayar sani ba". Ya ce: Ka ba ni labarin alamominta, ya ce: "Kuyanga za ta haifi uwargijiyarta, kuma za ka ga marasa takalma talakawa masu kiwon dabbobi suna gasar tsawaita gidaje", Ya ce: Sannan ya tafi, sai na zauna ɗan wani lokaci sannan ya ce da ni: "Ya Umar, shin ka san waye mai tambayar?" Na ce: Allah da Manzonsa ne mafi sani, ya ce: "To, lallai Jibrilu ne ya zo muku don ya sanar da ku addininku".
بَيْنَمَا نَحْنُ عِنْدَ رَسُولِ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ ذَاتَ يَوْمٍ إِذْ طَلَعَ عَلَيْنَا رَجُلٌ شَدِيدُ بَيَاضِ الثِّيَابِ، شَدِيدُ سَوَادِ الشَّعَرِ، لَا يُرَى عَلَيْهِ أَثَرُ السَّفَرِ، وَلَا يَعْرِفُهُ مِنَّا أَحَدٌ، حَتَّى جَلَسَ إِلَى النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ، فَأَسْنَدَ رُكْبَتَيْهِ إِلَى رُكْبَتَيْهِ، وَوَضَعَ كَفَّيْهِ عَلَى فَخِذَيْهِ، وَقَالَ: يَا مُحَمَّدُ، أَخْبِرْنِي عَنِ الْإِسْلَامِ، فَقَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «الْإِسْلَامُ أَنْ تَشْهَدَ أَنْ لَا إِلَهَ إِلَّا اللهُ، وَأَنَّ مُحَمَّدًا رَسُولُ اللهِ، وَتُقِيمَ الصَّلَاةَ، وَتُؤْتِيَ الزَّكَاةَ، وَتَصُومَ رَمَضَانَ، وَتَحُجَّ الْبَيْتَ إِنِ اسْتَطَعْتَ إِلَيْهِ سَبِيلًا» قَالَ: صَدَقْتَ، قَالَ: فَعَجِبْنَا لَهُ، يَسْأَلُهُ وَيُصَدِّقُهُ، قَالَ: فَأَخْبِرْنِي عَنِ الْإِيمَانِ، قَالَ: «أَنْ تُؤْمِنَ بِاللهِ، وَمَلَائِكَتِهِ، وَكُتُبِهِ، وَرُسُلِهِ، وَالْيَوْمِ الْآخِرِ، وَتُؤْمِنَ بِالْقَدَرِ خَيْرِهِ وَشَرِّهِ» قَالَ: صَدَقْتَ، قَالَ: فَأَخْبِرْنِي عَنِ الْإِحْسَانِ، قَالَ: «أَنْ تَعْبُدَ اللهَ كَأَنَّكَ تَرَاهُ، فَإِنْ لَمْ تَكُنْ تَرَاهُ فَإِنَّهُ يَرَاكَ» قَالَ: فَأَخْبِرْنِي عَنِ السَّاعَةِ، قَالَ: «مَا الْمَسْؤُولُ عَنْهَا بِأَعْلَمَ مِنَ السَّائِلِ» قَالَ: فَأَخْبِرْنِي عَنْ أَمَارَتِهَا، قَالَ: «أَنْ تَلِدَ الْأَمَةُ رَبَّتَهَا، وَأَنْ تَرَى الْحُفَاةَ الْعُرَاةَ الْعَالَةَ رِعَاءَ الشَّاءِ يَتَطَاوَلُونَ فِي الْبُنْيَانِ» قَالَ: ثُمَّ انْطَلَقَ، فَلَبِثْتُ مَلِيًّا ثُمَّ قَالَ لِي: «يَا عُمَرُ، أَتَدْرِي مَنِ السَّائِلُ؟» قُلْتُ: اللهُ وَرَسُولُهُ أَعْلَمُ، قَالَ: «فَإِنَّهُ جِبْرِيلُ، أَتَاكُمْ يُعَلِّمُكُمْ دِينَكُمْ».
Umar ɗan Khaɗɗab - Allah Ya yarda da shi - yana ba da labari cewa Jibril - aminci ya tabbata a gare shi - ya fito wurin sahabbai - Allah Ya yarda da su - a surar wani mutum namiji ba a sanshi ba, daga siffofinsa, cewa tufafinsa masu tsananin fari ne, gashin kansa kuma mai tsananin baƙi ne, ba a ganin gurbin tafiya a gareshi na bayyanar gajiya, da ƙura, da rarrabewar gashi, da dattin tufafi, kuma wani ɗaya daga mahalartan bai sanshi ba, alhali su suna zaune a wurin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -, sai ya zauna a gaban Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - irin zaman mai neman sani, sai ya tambayeshi game da musulunci, sai ya ba shi amsa da waɗannan rukunan, waɗanda suka ƙunshi iƙirari da shaida biyu, da kiyayewa a kan salloli biyar, da ba da zakka ga waɗanda suka cancanta, da azimin watan Ramadan, da ba da farillar Hajji a kan mai iko. Sai mai tambayar ya ce: Ka yi gaskiya, sai sahabbai suka yi mamaki daga tambayarsa mai nuni a kan rashin saninsa a cikin abin da yake bayyana da kuma gasgatashi. Sannan ya tambaye shi gami da imani, sai ya amsa masa da waɗannan rukunan guda shida masu ƙunshe da imani da samuwar Allah - Maɗaukakin sarki - da siffofinsa, da kaɗaitashi da ayyukansa kamar halitta, da kaɗaita shi da ibada, kuma cewa mala'iku waɗanda Allah Ya haliccesu daga haske bayi ne ababen girmamawa ba sa saɓawa Allah - Maɗaukakin sarki - kuma suna aiki da umarninsa, da yin imani da littattafan da aka saukar ga manzanni daga Allah - maɗaukakin sarki -, kamar Alƙur'ani da At-Taura da Linjila da wasunsu, da kuma (imani) da manzanni masu isar da Addinin Allah, daga cikinsu akwai (annabi) Nuhu, da Ibrahim, da Musa, da Isa, da na ƙarshensu (annabi) Muhammad - tsira da amincin Allah su tabbata a gare su -, da wasunsu daga cikin Annabawa da manzanni, da imani da ranar lahira, abin da ke bayan mutuwa yana shiga cikinsu na kabari da rayuwar barzahu, kuma cewa mutum za a tasheshi bayan mutuwa kuma za a yi masa hisabi, kuma makomarsa za ta zama ko dai zuwa aljanna ko zuwa wuta, da imani da cewa Allah Ya ƙaddara abubuwa gwargwadon yadda iliminsa ya rigaya da shi, kuma hikimarsa ta hukuntashi da rubutunsa ga hakan, da mashi'arsa gareshi, da afkuwarsu gwargwadon yadda ya ƙaddarasu, ya kuma haliccesu don haka. Sannan ya tambaye shi game da kyautatawa, sai ya ba shi labari da cewa kyautatawa ita ce ya bautawa Allah kamar shi yana ganinsa, idan bai samu damar kaiwa zuwa wannan matsayin ba, to, ya bautawa Allah - Maɗaukakin sarki - kamar Allah Yana ganinisa, na farko shi ne matsayin Mushahada, ita ce mafi ɗaukaka, na biyu shi ne matsayin Muraƙabah. Sannan ya tambaye shi yaushe ne alƙiyama? sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya bayyana cewa sanin al-ƙiyama yana daga abin da Allah Ya keɓanta da saninsa, babu wani daga halitta da ya sanshi, wanda ake tambayar da mai tambayar. Sannan ya tambaye shi gami da alamomin alƙiyama? Sai ya bayyana masa cewa daga cikin alamominta akwai yawan kuyangi (sa-ɗaka) da 'ya'yansu, ko yawan saɓawar 'ya'ya ga iyayensu, mata za su dinga yi musu mu'amala irirn mu'amalar bayi, kuma cewa makiyaya dabbobi da talakawa za a shinfiɗa musu duniya a ƙarshen zamani, sai su dinga alfahari a ƙawata gine-gine da ɗaukakasu. Sannan Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ba da labari da cewa mai tambayar shi ne Jibrilu ya zo don sanar da sahabbai wannan addinin miƙaƙƙe.
...:
Kyawawan ɗabi'un Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -, kuma yana zama tare da sahabbansa su ma suna zama a wurinsa.
Halaccin tausasawa ga mai tambaya da kusanto da shi, don ya samu damar tambaya ba tare da takura ko tsoro ba.
Ladabi tare da malami kamar yadda Jibril - aminci ya tabbata a gare shi - ya yi, yayin da ya zauna a gaban Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - irin zaman mai ladabi don ya karɓa daga gareshi.
Rukunan musulumci guda biyar ne, kuma rukunan imani guda shida ne.
Yayin haɗuwar musulunci da imani ana fassara musulunci da al'amura na zahiri, imani kuma da al'amura na baɗini.
Bayanin cewa addini darajoji ne mabanbanta, daraja ta farko: Musulunci, ta biyu: Imani, ta uku: Kyautatawa, ita ce ƙololuwarsu.
Asali ga mai tambaya shi ne rashin ilimi, jahilci shi ne mai sa tambaya, saboda haka sahabbai suka yi mamaki game da tambayarsa da gasgatawarsa.
Farawa da mafi muhimmanci sannan mai bi masa; domin an fara da shahada biyu wajen fassara musulunci, kuma anfara da imani da Allah a fassarar imani.
Tambayar ma'abota ilimi abin da mai tambaya bai jahilceshi ba, don ya sanar da waninsa.
Sanin alƙiyama yana daga abin da Allah Ya keɓanta da saninsa.
Sahih Muslim (1/ 36) (8).
Kari (9)
التحفة الربانية في شرح الأربعين حديثا النووية (ص7).
شرح الأربعين النووية.
لابن عثيمين (ص19).
فتح القوي المتين في شرح الأربعين وتتمة الخمسين.
للعباد (ص15).
الأحاديث الأربعون النووية وعليها الشرح الموجز المفيد.
لعبد الله المحسن (ص7).
تاج العروس من جواهر القاموس.
للزبيدي (2/ 460).
An ambata a cikin littattafai
48 Littattafai- AƘIDA INGANTACCIYAدروس العقيدة الصحيحة«To ka bani labari game da imani, ya ce: Ka bada gaskiya da Allah, da Mala'ikunSa, da littattafanSa, da ManzanninSa, da ranar lahira, kuma ka yi imani da ƙaddara alherinta da kuma sharrinta».
- TUSHE GUDA UKU DA DALILANSUYa ce: Ka bautawa Allah kamar kana ganinSa, idan kai ba ka ganinSa, to Shi Yana ganinka.
- TUSHE GUDA UKU DA DALILANSUSai ya ce: Wanda ake tambaya bai fi wanda yake tambayar sani ba.
- Imanin da Allah wanda Ya wajabta shi akan bayinSa daga abinda ya zo a cikin Alkur'ani mai girma da Sunnar Annabta.Daga Umar Dan Khattab, Allah ya yarda da shi ya ce; Wata rana muna zaune a wurin Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yayin da wani mutum ya ɓullo mana mai tsananin farin tufafi, mai tsananin baƙin gashi, ba a ganin
- Imanin da Allah wanda Ya wajabta shi akan bayinSa daga abinda ya zo a cikin Alkur'ani mai girma da Sunnar Annabta."Ka yi imani da Allah da mala’ikunSa da littattafanSa da manzanninSa, da ranar lahira, kuma ka yi imani da ƙaddara alherinsa da sharrinsa'. Ya ce: Ka yi gaskiya.
- TAƘAITACCEN BAYANI A KAN AƘIDAR MUSULUNCIنبذة في العقيدة الإسلامية«Imani: (shi ne) ka yi imani da Allah, da mala'ikunSa, da littattafanSa, da ManzanninSa, da ranar lahira, kuma ka yi imani da ƙaddara: alkhairinta da sharrinta» [3].
Kari (42)
- الإسلام أصوله ومبادئه(الإسلام أن تشهد أن لا إله إلا الله، وأن محمداً رسول الله، وتقيم الصلاة وتؤتي الزكاة، وتصوم رمضان، وتحج البيت إن استطعت إليه سبيلاً) [197]،
- الإسلام دين كامل«هُوَ أَنْ تَعْبُدَ اللَّهَ كَأَنَّكَ تَرَاهُ، فَإِنْ لَمْ تَكُنْ تَرَاهُ فَإِنَّهُ يَرَاكَ» [1].
- الخطب المنبريةموسوعة الخطب المنبرية (القسم الأول)«الْإِحْسَانَ: أَنْ تَعْبُدَ اللَّهَ كَأَنَّكَ تَرَاهُ، فَإِنْ لَمْ تَكُنْ تَرَاهُ فَإِنَّهُ يَرَاكَ»
- الخطب المنبرية موسوعة الخطب المنبرية (القسم الثاني)«أَنْ تَعْبُدَ اللَّهَ كَأَنَّكَ تَرَاهُ، فَإِنْ لَمْ تَكُنْ تَرَاهُ فَإِنَّهُ يَرَاكَ»"
- الخطب المنبريةموسوعة الخطب المنبرية (القسم الثالث)«الْإِحْسَانُ أَنْ تَعْبُدَ اللَّهَ كَأَنَّكَ تَرَاهُ، فَإِنْ لَمْ تَكُنْ تَرَاهُ فَإِنَّهُ يَرَاكَ»
- العلم الواجب بدون فقه وبدون زيادات1(أَن تُؤْمِنَ بِاللهِ، وَمَلَائِكَتِهِ، وَكُتُبِهِ، وَرُسُلِهِ، وَالْيَوْمِ الآخِرِ، وَتُؤْمِنَ بِالْقَدَرِ خَيْرِهِ وَشَرِّهِ).
- العلم الواجب بدون فقه وبدون زيادات1(أَن تَعْبُدَ اللهَ كَأَنَّكَ تَرَاهُ، فَإِن لَّمْ تَكُن تَرَاهُ فَإِنَّهُ يَرَاكَ).
- الله -جل جلاله- أنيس المحبين وملاذ القاصدين«أَنْ تَعْبُدَ اللهَ كَأَنَّكَ تَرَاهُ، فَإِنَّ لَمْ تَكُنْ تَرَاهُ فَإِنَّهُ يَرَاكَ»
- الله -جل جلاله- أنيس المحبين وملاذ القاصدين«أَنْ تُؤْمِنَ بِاللهِ، وَمَلَائِكَتِهِ، وَكُتُبِهِ، وَرُسُلِهِ، وَاليَوْمِ الآخِرِ، وَتُؤْمِنَ بِالقَدَرِ خَيْرِهِ وَشَرِّهِ»
- الله -جل جلاله- أنيس المحبين وملاذ القاصدين«أَنْ تَعْبُدَ اللهَ كَأَنَّكَ تَرَاهُ، فَإِنْ لَمْ تَكُنْ تَرَاهُ فَإِنَّهُ يَرَاكَ»
- الله -جل جلاله- أنيس المحبين وملاذ القاصدين«أَنْ تَعْبُدَ اللهَ كَأَنَّكَ تَرَاهُ، فَإِنَّ لَمْ تَكُنْ تَرَاهُ فَإِنَّهُ يَرَاكَ»
- الله -جل جلاله- أنيس المحبين وملاذ القاصدين«أَنْ تَعْبُدَ اللهَ كَأَنَّكَ تَرَاهُ، فَإِنَّ لَمْ تَكُنْ تَرَاهُ فَإِنَّهُ يَرَاكَ»
- المناهج التعليمية - الصف السادسالمناهج الدراسية - الفقه - الصف السادس «الإِسْلَامُ أَنْ تَشْهَدَ أَنْ لَا إِلَهَ إِلَّا اللهُ، وَأَنَّ مُحَمَّدًا رَسُولُ اللهِ، وَتُقِيمَ الصَّلَاةَ، وَتُؤْتِيَ الزَّكَاةَ، وَتَصُومَ رَمَضَانَ، وَتَحُجَّ الْبَيْتَ إِنِ اسْتَطَعْتَ إِلَيْهِ سَبِيلًا»[9].
- المناهج التعليمية - الصف السادسالمناهج الدراسية - الفقه - الصف السادس «الإِسْلَامُ أَنْ تَشْهَدَ أَنْ لَا إِلَهَ إِلَّا اللهُ، وَأَنَّ مُحَمَّدًا رَسُولُ اللهِ، وَتُقِيمَ الصَّلَاةَ، وَتُؤْتِيَ الزَّكَاةَ، وَتَصُومَ رَمَضَانَ، وَتَحُجَّ الْبَيْتَ إِنِ اسْتَطَعْتَ إِلَيْهِ سَبِيلًا»[24].
- حراسة التوحيدالعقيدة الصحيحة وما يضادها «الإِيمَانُ أَنْ تُؤْمِنَ بِاللَّهِ، وَمَلَائِكَتِهِ، وَكُتُبِهِ، وَرُسُلِهِ، وَاليَوْمِ الآخِرِ، وَتُؤْمِنَ بِالقَدَرِ خَيْرِهِ وَشَرِّهِ»[1].
- خذ عقيدتك من الكتاب والسنة الصحيحة"الإسلام أن تشهد أن لا إله إِلا الله وأن محمدًا رسول الله، وتُقيم الصلاة، وتؤتي الزَّكاة، وتصوم رمضان، وتَحجَّ البيت إن استطعت إليه سبيلًا".
- خذ عقيدتك من الكتاب والسنة الصحيحة"الإيمان: أن تؤمن باللهِ، وملائكتِه وكتبه، ورسلِه، واليوم الآخر، وتؤمن بالقدَر خيره وشره"
- خذ عقيدتك من الكتاب والسنة الصحيحة«الإحسان أن تعبدَ الله كأنك تراه، فإن لم تكن تراهُ فإنه يَرَاك»
- خطبة عرفة(الإِسْلاَمُ أَنْ تَشْهَدَ أَنْ لا إِلَهَ إِلَّا اللهُ وَأَنَّ مُحَمَّدًا رَسُولُ اللهِ، وَتُقِيمَ الصَّلَاةَ، وَتُؤْتِيَ الزَّكَاةَ، وَتَصُومَ رَمَضَانَ، وَتَحُجَّ الْبَيْتَ إِنِ اسْتَطَعْتَ إِلَيْهِ سَبِيلًا).
- رياض الصالحينرياض الصالحين مع فوائد وهدايات - 1 «بَيْنَمَا نَحْنُ جُلُوسٌ عِنْدَ رسولِ الله صلى الله عليه وسلم ، ذَاتَ يَوْمٍ إذْ طَلَعَ عَلَيْنَا رَجُلٌ شَديدُ بَياضِ الثِّيَابِ، شديدُ سَوَادِ الشَّعْرِ، لا يُرَىٰ عَلَيْهِ أَثرُ السَّفَرِ، وَلا يَعْرِفُهُ منَّا أحَدٌ، حَتَّىٰ جَلَسَ إلَ
- سؤال وجواب حول الإسلام«الإِحْسَانُ أَنْ تَعْبُدَ اللَّهَ كَأَنَّكَ تَرَاهُ، فَإِنْ لَمْ تَكُنْ تَرَاهُ فَإِنَّهُ يَرَاكَ»
- شرح الأصول الثلاثة«أَنْ تَعْبُدَ اللَّهَ كَأَنَّكَ تَرَاهُ» [21]
- شرح الأصول الثلاثةقَالَ: فَأَخْبِرْنِي عَنِ الإِيمَانِ؟ قَالَ: «أَنْ تُؤْمِنَ بِاللَّهِ، وَمَلَائِكَتِهِ، وَكُتُبِهِ، وَرُسُلِهِ، وَالْيَوْمِ الآخِرِ، وَتُؤْمِنَ بِالْقَدَرِ خَيْرِهِ وَشَرِّهِ» قَالَ: صَدَقْتَ.
- عقيدة الأئمة الأربعة«أَنْ تُؤْمِنَ بِاللَّهِ، وَمَلَائِكَتِهِ، وَكُتُبِهِ، وَرُسُلِهِ، وَالْيَوْمِ الآخِرِ، وَتُؤْمِنَ بِالْقَدَرِ خَيْرِهِ وَشَرِّهِ»
- فضل الإسلام{ الإسلام أن تشهد أن لا إله إلا الله، وأن محمدا رسول الله، وتقيم الصلاة، وتؤتي الزكاة، وتصوم رمضان، وتحج البيت إن استطعت إليه سبيلا } [8].
- قاموس الكبائر موسوعة الكبائر - المجموعة الأولى«أَنْ تَعْبُدَ اللهَ كَأَنَّكَ تَرَاهُ، فَإِنْ لَمْ تَكُنْ تَرَاهُ، فَإِنَّهُ يَرَاكَ» [50].
- قاموس الكبائر«أَنْ تَعْبُدَ اللهَ كَأَنَّكَ تَرَاهُ، فَإِنْ لَمْ تَكُنْ تَرَاهُ، فَإِنَّهُ يَرَاكَ» [50].
- كيف أكون مسلمًا؟1(الإِسْلاَمُ أَنْ تَشْهَدَ أَنْ لاَ إِلَهَ إِلاَّ اللَّهُ وَأَنَّ مُحَمَّدًا رَسُولُ اللهِ، وَتُقِيمَ الصَّلاَةَ، وَتُؤْتِيَ الزَّكَاةَ، وَتَصُومَ رَمَضَانَ، وَتَحُجَّ الْبَيْتَ إِنِ اسْتَطَعْتَ إِلَيْهِ سَبِيلًا)
- ما لا يسع أطفال المسلمين جهله«فَأَخْبِرْنِي عَنِ الإِيمَانِ، قَالَ: أَنْ تُؤْمِنَ بِاللهِ، وَمَلَائِكَتِهِ، وَكُتُبِهِ، وَرُسُلِهِ، وَاليَوْمِ الآخِرِ، وَتُؤْمِنَ بِالقَدَرِ خَيْرِهِ وَشَرِّهِ»[3].
- مادة العقيدة الإسلامية(أن تؤمن بالله، وملائكته، وكتبه، ورسله، واليوم الآخر، وتؤمن بالقدر خيره وشره).[65]
- مادة العقيدة الإسلامية(قَالَ فأخبرني عَنِ السَّاعَةِ. قَالَ مَا الْمَسْئُولُ عَنْهَا بِأَعْلَمَ مِنَ السَّائِلِ. قَالَ فأخبرني عَنْ أَمَارَتِهَا. قَالَ أَنْ تَلِدَ الأَمَةُ رَبَّتَهَا، وَأَنْ تَرَى الْحُفَاةَ الْعُرَاةَ الْعَالَةَ رِعَاءَ الشَّاءِ يَتَطَاوَلُونَ
- مجموعة زاد التفسير (2)التفسير 2«ما المسْؤُولُ عَنْها بأعْلَمَ من السَّائلِ».
- مجموعة زاد الحديث (1)الحديث 1قَالَ: بَيْنَمَا نَحْنُ عِنْدَ رَسُولِ الله صلى الله عليه وسلم ذَاتَ يَوْمٍ، إِذْ طَلَعَ عَلَيْنَا رَجُلٌ شَدِيدُ بَيَاضِ الثِّيَابِ، شَدِيدُ سَوَادِ الشَّعَرِ، لَا يُرَى عَلَيْهِ أَثَرُ السَّفَرِ، وَلَا يَعْرِفُهُ مِنَّا أَحَدٌ، حَتَّى جَل
- مشروع المنهج التعليميمادة التوحيد مستوى 2«الْإِسْلَامُ أَنْ تَشْهَدَ أَنْ لَا إِلَهَ إِلَّا اللهُ وَأَنَّ مُحَمَّدًا رَسُولُ اللهِ ﷺ وَتُقِيمَ الصَّلَاةَ، وَتُؤْتِيَ الزَّكَاةَ، وَتَصُومَ رَمَضَانَ، وَتَحُجَّ الْبَيْتَ إِنِ اسْتَطَعْتَ إِلَيْهِ سَبِيلًا»، قَالَ: صَدَقْتَ، قَالَ: ف
- مشروع منهاج زادكزادك 1 طالببَيْنَمَا نَحْنُ عِنْدَ رَسُولِ اللهِ صلى الله عليه وسلم ذَاتَ يَوْمٍ، إِذْ طَلَعَ عَلَيْنَا رَجُلٌ شَدِيدُ بَيَاضِ الثِّيَابِ، شَدِيدُ سَوَادِ الشَّعَرِ، لَا يُرَى عَلَيْهِ أَثَرُ السَّفَرِ، وَلَا يَعْرِفُهُ مِنَّا أَحَدٌ، حَتَّى جَلَسَ إِ
- نبراس طالب (1)1«أَنْ تُؤْمِنَ بِاللهِ، وَمَلَائِكَتِهِ، وَكُتُبِهِ، وَرُسُلِهِ، وَالْيَوْمِ الْآخِرِ، وَتُؤْمِنَ بِالْقَدَرِ خَيْرِهِ وَشَرِّهِ»، قَالَ: صَدَقْتَ.
- نبراس طالب (1)1«الْإِسْلَامُ أَنْ تَشْهَدَ أَنْ لَا إِلَهَ إِلَّا اللهُ وأَنَّ مُحَمَّدًا رَسُولُ اللهِ، وَتُقِيمَ الصَّلَاةَ، وَتُؤْتِيَ الزَّكَاةَ، وَتَصُومَ رَمَضَانَ، وَتَحُجَّ الْبَيْتَ إِنِ اسْتَطَعْتَ إِلَيْهِ سَبِيلًا».
- نبراس طالب (1)1«أَنْ تُؤْمِنَ بِاللهِ، وَمَلَائِكَتِهِ، وَكُتُبِهِ، وَرُسُلِهِ، وَالْيَوْمِ الْآخِرِ، وَتُؤْمِنَ بِالْقَدَرِ خَيْرِهِ وَشَرِّهِ».
- نبراس طالب (1)1«أَنْ تَعْبُدَ اللهَ كَأَنَّكَ تَرَاهُ، فَإِنْ لَمْ تَكُنْ تَرَاهُ فَإِنَّهُ يَرَاكَ».
- نبراس طالب (1)1«أَنْ تَعْبُدَ اللهَ كَأَنَّكَ تَرَاهُ، فَإِنْ لَمْ تَكُنْ تَرَاهُ فَإِنَّهُ يَرَاكَ»
- نبراس طالب (2)نبراس طالب (2) «أَنْ تَعْبُدَ اللهَ كَأَنَّكَ تَرَاهُ، فَإِنْ لَمْ تَكُنْ تَرَاهُ فَإِنَّهُ يَرَاكَ»
- نبراس طالب (3)نبراس طالب 3«أَنْ تَعْبُدَ اللهَ كَأَنَّكَ تَرَاهُ، فَإِنْ لَمْ تَكُنْ تَرَاهُ فَإِنَّهُ يَرَاكَ»