Skip to content
Jerin Surori /

الطَّارق

الطَّارق is chapter 86 of the Quran and has 17 verses. This page presents it in full in the Uthmani script, with a verse-by-verse translation of its meaning.

17 Ayoyi Lambar Sura 86
Je zuwa aya
Hausa · Gummi
بِسْمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحْمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ

وَٱلسَّمَآءِ وَٱلطَّارِقِ

Inã rantsuwa da sama da mai aukõwa da dare.

وَمَآ أَدۡرَىٰكَ مَا ٱلطَّارِقُ

To, mẽ yã sanar da kai abin da ake cẽwa mai aukõwa da dare?

ٱلنَّجۡمُ ٱلثَّاقِبُ

Shi ne taurãron nan mai tsananin haske.

Explanation & meanings · 1
  1. Wannan ya yi kama da zuwan Annabi a cikin jahiliyya don ya haskaka duniya da ilimi kamar yadda girgije ke ba da ruwa saboda tsiron ƙasa, hantsar uwa ta ba da nono saboda jariri kuma maniyi ya zo lokacin Jima'i.

إِن كُلُّ نَفۡسٖ لَّمَّا عَلَيۡهَا حَافِظٞ

Bãbu wani rai fãce a kansa akwai wani mai tsaro.

فَلۡيَنظُرِ ٱلۡإِنسَٰنُ مِمَّ خُلِقَ

To, mutum ya dũba, daga mẽ aka halittã shi?