Skip to content
Jerin Surori /

البُرُوج

البُرُوج is chapter 85 of the Quran and has 22 verses. This page presents it in full in the Uthmani script, with a verse-by-verse translation of its meaning.

22 Ayoyi Lambar Sura 85
Je zuwa aya
Hausa · Gummi
بِسْمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحْمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ

وَٱلسَّمَآءِ ذَاتِ ٱلۡبُرُوجِ

Inã rantsuwa da sama mai taurãrin lissafin shekara.

وَٱلۡيَوۡمِ ٱلۡمَوۡعُودِ

Da yinin da aka yi alkawarin zuwansa,

Explanation & meanings · 1
  1. Rãnar Ƙiyãma.

وَشَاهِدٖ وَمَشۡهُودٖ

Da yini mai shaidu, da yini da ake halarta a cikinsa

Explanation & meanings · 1
  1. Rãnar Arafa.

قُتِلَ أَصۡحَٰبُ ٱلۡأُخۡدُودِ

An la'ani mutãnen rãmi.

Explanation & meanings · 1
  1. Mutãnen Najiran ne suka yi rãmi suka hũra wuta a ciki, dõmin su ƙõne wanda yã yi ĩmãni da addinin Masĩh Ĩsa dõmin su hana yãɗuwarsa. Suka umurci kõwane Musulmi ya jefa kansa a ciki, su kuma suna zazzaune suna kallo.

ٱلنَّارِ ذَاتِ ٱلۡوَقُودِ

Wato wuta wadda aka hura.