Skip to content

Kwatankwacin muminai a soyayyarsu da jinkansu da tausayinsu tamkar jiki ne, idan wata gaba daga gare shi ta yi ciwo sai ragowar jikin ya dauka da rashin bacci da zazzabi

Daga Nu'uman Dan Bashir - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce:

"Kwatankwacin muminai a soyayyarsu da jinkansu da tausayinsu tamkar jiki ne, idan wata gaba daga gare shi ta yi ciwo sai ragowar jikin ya dauka da rashin bacci da zazzabi".

«مَثَلُ الْمُؤْمِنِينَ فِي تَوَادِّهِمْ وَتَرَاحُمِهِمْ وَتَعَاطُفِهِمْ مَثَلُ الْجَسَدِ، إِذَا اشْتَكَى مِنْهُ عُضْوٌ تَدَاعَى لَهُ سَائِرُ الْجَسَدِ بِالسَّهَرِ وَالْحُمَّى».

Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Ingantacce ne
Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana cewa yana wajaba halin musulmai sashinsu tare da sashi ya zama da son alheri da tausayi da taimakekeniya da taimako, da jin zafin abinda ya faru gare su na cuta kamar jiki daya ne, idan wata gaba ta yi rashin lafiya daga gare shi , sai jikin ya dauka gaba dayansa da rashin bacci da zazzabi.

Ma"anonin Kalmomi

...:

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

Yana kamata girmama hakkokin musulmai da kwadaitarwa akan taimakekeniyarsu da tausayin junansu.

Yana kamata soyayya da taimako su kasance tsakanin ma'abota imani.

Manazarta

Sahih Al-Bukhari (8/ 10) (6011).

Sahih Muslim (4/ 1999) (2586).

Kari (9)

نزهة المتقين شرح رياض الصالحين.

مجموعة من الباحثين (1/ 246).

بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين.

لسليم الهلالي (1/ 317).

كنوز رياض الصالحين.

مجموعة من الباحثين (4/ 405).

تطريز رياض الصالحين.

لفيصل آل مبارك (ص173).

المعجم الوسيط (1/ 492).