Skip to content
839 Hadisai

Kundin Hadisan Annabi

Tace sakamako

39 daga cikin katuna 839

Cire tacewa
«Abubuwa huɗu wanda ya kasance a cikinsu to ya kasance munafiki, idan akwai wata ɗabi'a daga cikinsu a tare da shi to ya kasance yana da ɗabi'ar munafunci har sai ya barta: Wanda idan zai yi zance sai ya yi ƙarya, idan ya yi alƙawari sai ya saɓa, idan aka yi rigima da shi sai ya yi fajirci, idan aka yi yarjejeniya da shi sai ya yi yaudara».
Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka ruwaito shi
"Shaidan yana zo wa dayanku sai ya ce: Waye ya halicci kaza? waye ya halicci abu kaza? har ya ce: Waye ya halicci Ubanugijinka? idan ya ga haka to (sai) ya nemi tsarin Allah ya kuma hanu".
Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
"Wanda ya rantse da amana to baya daga cikinmu".
Ingantacce ne Abu Dawud ne ya Rawaito shi da Kuma Ahmad
Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce wa Mu'azu Dan Jabal, lokacin da ya aike shi zuwa Yaman: "Lallai kai zaka je wa wasu mutane mazowa littafi, idan ka je musu to ka kirayesu zuwa su shaida cewa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, kuma cewa Annabi Muhammad Manzon Allah ne, idan su sun bika a kan hakan, to ka sanar da su cewa Allah Ya wajabta musu salloli biyar a kowanne yini da dare, idan su sun bika da hakan, to ka sanar da su cewa Allah Ya wajabta musu sadaka da za'a karba daga mawadatan su sai a dawo da ita ga talakawansu, idan su sun bika da hakan, to na haneka da manyan dukiyoyin su, ka tsoraci addu'ar wanda aka zalinta, lallai cewa ita babu wani shamaki tsakanin ta da Allah".
Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
"Abu biyu a cikin mutane su kafirci ne a cikinsu: Sukar nasaba, da kukan kera ga mamaci".
Ingantacce ne Muslim ne ya rawaito shi
"Lallai Allah ba ya zalintar mumini wani kyakkyawa, za'a ba shi a duniya kuma za’a yi masa sakayya da ita a lahira. Amma kafiri sai a ciyar da shi da kyakkyawan abinda ya aikata saboda Allah a duniya, har idan ya tafi lahira, (zai zama) ba shi da wani kyakkyawa da za’a yi masa sakayya da shi".
Ingantacce ne Muslim ne ya rawaito shi
"An gina Musulunci abisa abubuwa biyar, shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, kuma Annabi Muhammadu bawanSa ne kuma manzonSa ne, da tsaida sallah, da bada zakka, da ziyarar daki, da azimin Ramadan".
Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
'Misalin munafiki, kamar akuya ce mai kaikawo tsakanin turke biyu, tana kaikawo gurin wadannan wani lokaci da kuma zuwa wadancan a wani lokacin".
Ingantacce ne Muslim ne ya rawaito shi