Lallai cewa mafi sauƙin 'yan wuta a azaba wanda yake da takalma biyu da igiyoyi na wuta, ƙwaƙwalwarsa tana tafarfasa kamar yadda (tukunyar) tagulla take tafarfasa, ba ya ganin cewa wani mutum ya fi shi tsananin azaba, kuma shi shi ne mafi sauƙin azabarsu
Daga Nu'uman Dan Bashir - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce:
"Lallai cewa mafi sauƙin 'yan wuta a azaba wanda yake da takalma biyu da igiyoyi na wuta, ƙwaƙwalwarsa tana tafarfasa kamar yadda (tukunyar) tagulla take tafarfasa, ba ya ganin cewa wani mutum ya fi shi tsananin azaba, kuma shi shi ne mafi sauƙin azabarsu"
«إِنَّ أَهْوَنَ أَهْلِ النَّارِ عَذَابًا مَنْ لَهُ نَعْلَانِ وَشِرَاكَانِ مِنْ نَارٍ، يَغْلِي مِنْهُمَا دِمَاغُهُ كَمَا يَغْلِ الْمِرْجَلُ، مَا يَرَى أَنَّ أَحَدًا أَشَدُّ مِنْهُ عَذَابًا، وَإِنَّهُ لَأَهْوَنُهُمْ عَذَابًا».
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa mafi sauƙin 'yan wuta a azaba a ranar lahira wanda yake da takalma biyu da igiyoyi biyu ƙwaƙwalwarsa tana tafarfasa saboda zafinsu, kamar yadda tukunyar tagulla take tafarfasa, kuma ba ya ganin wani mutum ya fi shi tsananin azaba, kuma shi ne mafi sauƙin azabarsu, hakan dan azabar jiki da ta rai su haɗu a kansa.
Tsoratar da masu saɓo da kafirai daga tsoron wannan azabar a cikin wuta; dan su nisanci abinda zai kai zuwa gareta.
Banbacin matsayin masu shiga wuta gwargwadan mummunar ayyukansu.
Tsananin azabar wuta, Allah - Maɗaukakin sarki - Ya kuɓutar da mu daga gareta.
Sahih Al-Bukhari (8/ 115) (6561).
Sahih Muslim (1/ 196) (213).
Kari (9)
نزهة المتقين شرح رياض الصالحين.
لمجموعة من الباحثين (1/ 366).
كنوز رياض الصالحين.
لمجموعة من الباحثين (6/ 394).
بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين.
لسليم الهلالي (1/ 472).
شرح رياض الصالحين.
لابن عثيمين (3/ 295).
المعجم الوسيط (1/ 256).