Skip to content

Wannan kalmar ta gaske aljani ya fauceta ne, sai ya yi kyarkyararta a kunnen abokin harkarsa irin kyarkyarar kaza, sai su cakuɗata da ƙarya sama da ɗari

Daga Nana A'isha - Allah Ya yarda da ita - ta ce:

Wasu mutane sun tambayi Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi dangane da bokaye, sai Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: "Su ba komai ba ne". Suka ce: Ya Ma’aikin Allah; Wani lokacin suna ba da labari sai kuma abin ya zama gaske. Sai Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce; Wannan kalmar ta gaske aljani ya fauceta ne, sai ya yi kyarkyararta a kunnen abokin harkarsa irin kyarkyarar kaza, sai su cakuɗata da ƙarya sama da ɗari.

سَأَلَ أُنَاسٌ رَسُولَ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ عَنِ الْكُهَّانِ، فَقَالَ لَهُمْ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «لَيْسُوا بِشَيْءٍ» قَالُوا: يَا رَسُولَ اللهِ، فَإِنَّهُمْ يُحَدِّثُونَ أَحْيَانًا بِالشَّيْءِ يَكُونُ حَقًّا، فَقَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «تِلْكَ الْكَلِمَةُ مِنَ الْحَقِّ يَخْطَفُهَا الْجِنِّيُّ فَيَقُرُّهَا فِي أُذُنِ وَلِيِّهِ قَرَّ الدَّجَاجَةِ، فَيَخْلِطُونَ فِيهَا أَكْثَرَ مِنْ مِائَةِ كَذْبَةٍ».

Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Ingantacce ne
Bayani

An tambayi Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi dangane da waɗanda suke ba da labarin abin da zai faru nan gaba na gaibu, sai ya ce: Kada ku kula su, kada ku saurari maganarsu, kada ku shiga al’amarinsu. Sai suka ce: Maganarsu tana daidai da abin da ya faru a wani lokaci, kamar a ce su ba da labarin wani abu na gaibu zai faru a wata kaza a rana kaza, sai kuma ya faru kamar yadda suka faɗa. Sai Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: Aljanu suna sato abin da suke ji ne na labarun sama, sai su sauko da shi zuwa ga abokan hulɗarsu cikin bokaye, sai su ba su labarin abin da suka ji, sannan sai shi bokan ya ƙara ƙarya ɗari a kan wannan labarin da ya ji daga sama.

Ma"anonin Kalmomi

يخْطفُها: يأخذها بسرعة.

فَيَقُرُّهَا في أُذُنِ: يلْقِيهَا على مسَامِع.

قرَّ الدجاج: صوتها عند مخاطبة دجاجة أخرى.

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

An hana a gasgata bokaye, kuma abin da suke faɗa ƙarya ne, kuma ƙagaggen [zance ne] ko da wani lokacin ya zama gaskiya.

An tsare sama daga shaiɗanu da aiko Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da su ji wani abu na wahayi ko waninsa, sai dai wanda ya saci magana ya kuma tsira daga tauraron [harbosu].

Aljanu suna da abokan hulɗarsu cikin mutane

Manazarta

Sahih Al-Bukhari (8/ 47) (6213).

Sahih Muslim (4/ 1750) (2228).

Kari (9)

نزهة المتقين (2/ 1143).

كنوز رياض الصالحين.

لمجموعة من الباحثين (17/ 557).

بهجة الناظرين.

لسليم الهلالي (3/ 177).

مرقاة المفاتيح شرح مشكاة المصابيح.

لعلي القاري (7/ 2904).

شرح رياض الصالحين.

لابن عثيمين (6/ 404).