Skip to content
التوبَة /

Aya 100

9 : 100

Aya 100 of التوبَة (9 : 100). This page carries the verse in the Uthmani script with a translation of its meaning, at a stable URL that can be cited on its own.

التوبَة Ayoyi 129
9 : 100

وَٱلسَّٰبِقُونَ ٱلۡأَوَّلُونَ مِنَ ٱلۡمُهَٰجِرِينَ وَٱلۡأَنصَارِ وَٱلَّذِينَ ٱتَّبَعُوهُم بِإِحۡسَٰنٖ رَّضِيَ ٱللَّهُ عَنۡهُمۡ وَرَضُواْ عَنۡهُ وَأَعَدَّ لَهُمۡ جَنَّٰتٖ تَجۡرِي تَحۡتَهَا ٱلۡأَنۡهَٰرُ خَٰلِدِينَ فِيهَآ أَبَدٗاۚ ذَٰلِكَ ٱلۡفَوۡزُ ٱلۡعَظِيمُ

Kuma mãsu tsẽrẽwa na farko daga Muhãjirina da Ansar da waɗanda suka bi su da kyautatãwa, Allah Ya yarda daga gare su su kuma sun yarda daga gare Shi, kuma Ya yi mãsu tattalin gidãjen Aljanna; ¡õramu sunã gudãna a ƙarƙashinsu, suna madawwamã a cikinsu har abada. Wancan ne babban rabo mai girma.

Explanation & meanings · 1
  1. Yãƙin Tabũka ya kasa jama'ar Musulmi gwargwadon ĩmãninsu da ayyukansu da gabãtarsu a cikin addĩni, cikin darajõji da ɗabaƙõƙi. Darajar farko ita ce, Sahabban farko waɗanda suka tsere wa sauran mutãne ga shigã Musulunci da ƙarfin ĩmãni da yawan aiki da tsarkake zũciya ga aikin Allah.