19 : 55
وَكَانَ يَأۡمُرُ أَهۡلَهُۥ بِٱلصَّلَوٰةِ وَٱلزَّكَوٰةِ وَكَانَ عِندَ رَبِّهِۦ مَرۡضِيّٗا
Kuma yã kasance yanã umurnin mutãnens da salla da zakka. Kuma yã kasance yardajje a wurin Ubangijinsa.
Explanation & meanings · 1
- Mãtarsa da 'ya'yansa da Jurhum, yanã umurninsu da salla da zakka. Yanã wajaba ga mutum ya umurci iyalinsa da tsare haƙƙõƙin Allah.