19 : 16
وَٱذۡكُرۡ فِي ٱلۡكِتَٰبِ مَرۡيَمَ إِذِ ٱنتَبَذَتۡ مِنۡ أَهۡلِهَا مَكَانٗا شَرۡقِيّٗا
Kuma ka ambaci Maryamu a cikin Littãfi, a lõkacin da ta tsallake daga mutãnenta a wani wuri, a gẽfen gabas.
Explanation & meanings · 1
- An fãra da ƙissar Maryamu dõmin a nũna sakamakon da aka yi mata da sãmun ɗan kirki sabõda kasancewarta mutumiyar kirki, kuma da nũna cewa Annabi Ĩsa bã ɗan Allah ba ne.